Sarki Sanusi Zai Halarci Bikin Kaɗe-Kaɗen Gargajiya Na Reggae A Anambara

195

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi; Oba na Onacha, Alfred Achebe da sauran manyan sarakunan gargajiya da ƙwararru suna daga cikin baƙin da ake sa rana za su halarci Nigerian Reggae Festival, NRF, wani mashahurin bikin kaɗe-kaden gargajiya da za a yi a Awka, babban birnin jihar Anambara daga 28 ga Disamba, 2019 zuwa 30 ga Disamba, 2019.

Kwamishinan Harkokin Mazauna Ƙasashen Waje, Fasahar Cikin Gida, Al’adu da Yawan Buɗe Ido na Jihar Anambara, Barista Sally Mbanefo, wadda ya bayyana haka ga manema labarai ranar Alhamis a Awka, ya ce Bikin Kaɗe-Kaɗe na Reggae da Kula da Ma’aikatar Harkokin Mazauna Ƙasashen Waje, Fasahar Cikin Gida Al’adu ke shiryawa da haɗin kan Music Africa Foundation yana da nufin haɓɓaka zaman lafiya, haɗin kai da al’ada.

“Kiɗan Reggae na Najeriya biki ne da ake tsarawa don a kawo zaman lafiya da haɗin kai ga al’ummar Najeriya a kuma kawar da hare-haren ƙin jinin baƙi a ƙasashen Afirka. Reggae yana bunƙasa zaman lafiya, yana gina gadar soyayya da haɗin kai tsakanin ‘yan Najeriya da ‘yan Afirka. Wannan taro ne na gida wanda ya yi dai-dai da ƙudirin Gwamna Willie Obiano na inganta zaman lafiya daga tushe, kuma mu dawo da fasihan makaɗan Reggae da suke ƙasashen waje gida”, in ji Mista Mbanefo.

Da yake bada gudunmawa, Shugaban African Music Awake Foundation, Prince Emeka Ojukwu, ya tabbatar da cewa Reggae ya yi tasiri a kan mutane da dama, kasuwanni, kafafen watsa labarai da taruka, ya kuma kafa kansa a matsayin wani tubali na wayar da kan al’umma.

“Wannan zai zama wani dandali na musayar al’adu tsakanin ‘yan Caribbean, Jamaica, ‘yan Najeriya da ‘yan Afirka mazauna ƙasashen waje. Makaɗan Reggae na ƙasashen waje za su zo. Makaɗa Reggae na Najeriya da makaɗan Reggae na Afirka za su samu damar haɗa kai da su”, in ji shi.

Wasu daga cikin makaɗan da za su cashe a bikin su ne Pacino, B’Clean, Crucial Bankie, Heph B, Jennifer Lou, Ledo, Black Mojah, DJ Silentkilla, Karamel Singer, Big Bob, Ras Udara Most High, Lioness Front, Ras Julian, Black Omolo, Anaetoh Peter, Ital Sounds, Pupayanns”, in ji shi.

Cif Vincent Omoko, Shugaban African Music Awake Foundation, ya faɗa wa majiyarmu cewa kiɗan Reggae shi ne taro mafi kyau wajen sake haɗa kan ‘yan Afirka, ya wayar da kan matasa kan illar rikice-rikicen addini da na ƙabialanci, hare-hare, fashi da sauran munanan halaye.

Shi kuwa Basaraken Aro da yake ƙaramar hukumar Idemili ta Arewa, ya tabbatar da cewa sarakunan gargajiya a shirye suke su yi amfani da taron don haɗuwa da mutane dake ƙasa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan