Abubuwa 5 Da Ka Iya Cutar Da Sarki Sanusi A Sabuwar Dokar Masarautu

385

Tun lokacin da gwamnatin jihar Kano ta yanke shawarar cewa ba za ta ɗaukaka ƙara ba game da hukuncin 21 ga Nuwamba na Babbar Kotun Kano, wadda ta rushe sabbin masarautu huɗu da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ƙirƙira, manya-manyan kwamishinoni suke ta shirya tarukan ganawa don ƙirƙirar wata doka ‘mara kuskure’, sannan su gabatar ga Majalisar Dokokin Jihar Kano don zartarwa.

A ranar 8 ga watan Mayu, Gwamna Ganduje ya sanya hannu a kan wata doka mai cike da rikici, wadda ta bada damar kafa ƙarin masarautu huɗu da sarakuna masu daraja ta ɗaya a Bichi, Rano, Ƙaraye da Gaya.

Masu lura da al’amuran yau da kullum da ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Kano sun yi tsammanin cewa akwai wata mummunar manufa lokacin da Majalisar ta katse hutunta don nazarin wata dokar da za ta kafa Hukumar Tallafa wa Ilimi ta Jihar Kano.

‘Yan majalisu na jam’iyyar PDP a Majalisar sun buƙaci Kakakin Majalisar, Abdul’aziz Garba-Gafasa da ya ba su tabbacin cewa ba za a tattauna wani batu ba banda dokar ilimin.

“Tun da farko Kakakin Majalisar ya faɗa mana cewa an katse hutun ne don a yi muhawara sannan a zartar da Dokar Ilimi Kyauta, amma ‘yan kwanaki kaɗan bayan haka, sai gwamnatin jihar ta turo da wani ƙudiri kan ƙirƙirar sabbin masarautu”, wani ɗan majalisar da ba ya so a bayyana sunansa ya bayyana wa majiyarmu haka.

“Har yanzu ba mu duba ƙudirin ba saboda shugabannin majalisar suna tsare da ita kamar mallakinsu. Amma idan aka fito da ita, za mu iya ƙoƙarinmu wajen yin abinda mutane ke buƙata.

Kwafin ƙudirin da majiyarmu ta gani ya fito da a ƙalla manya-manyan wurare biyar waɗanda kai tsaye ko ba kai tsaye ba sun shafi Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, wanda yake takun saƙa da gwamnan.

Ikon Naɗa Masu Naɗa Sarki Da Sarkin Kansa

Koda yake bisa doka gwamna ne ke da ikon amincewa da sunan sarki da masu naɗa sarki suka ba shi shawara, a sabuwar dokar an ce:
“Gwamna, bisa neman shawarar Majalisar Sarakunan Kano, Bichi, Ƙaraye, Rano da Gaya zai naɗa wa masarautun masu naɗa sarki”.

Zai yiwu gwamna ya ajiye wannan iko idan masu naɗa Sarkin Kano- Madaki, Makama, Sarkin Bai da Sarkin Dawaki Maituta suka hau kujerar naƙi suka ce suna so a bar su a Kano, kuma za su iya kai gwamnati ƙara bisa ajiye su a ƙarƙashin sabbin masarautu.

Da alama Sashi na 25 na dokar za a yi amfani da shi ne don muzguna wa Sarki Sanusi, wanda a kwanakin baya Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi Da Cin Hanci ta Jihar Kano ta fara binciken sa bisa zargin kashe wasu kuɗaɗen Masarautar Kano ba bisa ka’ida ba.

Sashin yana cewa: “A ƙarshen kowace shekarar kuɗi, Kwanturola na kowace Masarauta zai shirya sannan ya miƙa kasafin kuɗin Masarautar na shekara mai zuwa ga gwamna domin sahalewa.

Gwamna Zai Iya Rage Muƙamin Sarki

Sashi na 12 na dokar ya ce:
“Gwamna zai iya mayar da sarki mai daraja ta ɗaya, mai daraja ta biyu ko mai daraja ta uku.

Koda yake dai majiyoyin cikin gida sun shaida wa majiyarmu cewa gwamnan yana neman “mafitar siyasa” ko “halin ka yi nasara na yi nasara” wajen rage darajar sarakunan zuwa muƙamin daraja ta biyu, abin da bai fito fili ba shi ne ko an yi wannan tanadin ne don a nufi Masarautar Kano.

Yawan Ikon Ganduje

Za a iya tumɓuke sarki idan ya gaza halartar tarukan Majalisar Sarakunan Kano, wadda ta ƙunshi masarautu biyar a jihar, Sakataren Gwamnatin Jiha, Kwamishinan Ƙananan Hukumomi, shugabanni ƙananan hukumomi guda biyar (ɗaya daga kowace Masarauta), masu naɗa sarki 10 (biyu daga kowace Masarauta), Babban Limamin kowace Masarauta, wakilin ‘yan kasuwa, wakilai biyu daga hukumomin tsaro (gwamna zai naɗa)

A cewar Sashi na 13 na dokar, gwamna, bayan cikakken bincike da neman shawarar Majalisar Sarakuna ta Jihar Kano, zai iya sauke kowane Sarki idan ya gamsu cewa:

(a) ana buƙatar saukewar bisa tanadin al’adu ko kuma ta wajaba don kare ɗabi’u da al’ada ko zaman lafiya, oda da kyakkyawan shugabanci

(b) inda sarki yana sane kuma da gangan ya ƙi halartar tarukan Majalisar Sarakuna ta Jihar Kano sau 3 a jere ba tare da ƙwaƙkwara kuma karɓaɓben dalili ba.

(c) inda sarki ya yi abin kunya; ko
(d) inda sarki ya ci mutuncin muƙami; ko

(e) inda sarki ya aikata wani abu na rashin tarbiyya ko ya yi wani abu ta hanyar ta ba ta dace ba, wanda bai ta yi dai-dai da halayen al’umma ba da kuma laduban wannan kujera

Sarakuna Za Su Ba Gwamna Shawara Ne Kawai Idan An Buƙace Su Su Yi Haka

A cewar Sashi na 6 (2) na dokar, “Majalisar, idan gwamna ya buƙace ta za ta iya ba shi shawara a kan:

“Duk wani al’amari da yake da dangantaka da kiyaye zaman lafiya a cikin jihar ko wani ɓangare na jihar; ko

(b) wasu al’amura da gwamnan zai iya bada umarni

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan