Takardu 6 Da Za Su Raba Ku Da Ƙalatar Jamian tsaro A Hanya

281

Takardu shida da zasu shiga stakanin ka da ma’aikata a yayin da ka ke bukar ku kasance a inda kuke so ba tare da muzgunawa ko bata lokaci bare ma akai ga yatsina gashin baki. Wanna takardu na da alfanu ga sabin matuka.
1 Lasisin tuki wadda akewa lakabi da driven license.


Ita ce takarda mafi amfani da duk ilahirin matuka dole su malaka daga hanun hukumar FRSC mai kula da dokokin hanya, abisa tsarin kasa ya zamo tilas ga wanda zai hau kan titi yayi tuki bayan kasancewa dan shakara 18, to kuma sai malaki wanan takarda ta lamincewa a tuki.


2 Takardar cancantar abin hauwa a bisa titi


Bayana malakar shedar tuki to lallai ne ga mai abin hauwa ya garzaya domin malakar takardar amincewa da cancantar abin haun sa yayi yawo a fadin titin kasar nan. Ana neman wanan izini ne daga hukumar VIO masu alhakin tabbatar cancantar kasancewar abin hauwa bisa titi.


3 Takardar inshora


Wanan takarda na taimakawa mai abin hauwa samun talafi ko sauki a yayin da wani haɗari ya auku da abin hauwa, ƙonewa, shin karo ne, gogewar jikin mota ne, ko hautsinaw abin hauwa yayi. Ita wanan takarda ce zata taka muhimmiyar rawa wajen ganin cewa mai abin hauwa ya samu an biya ko sauya masa abin hauwan muddin yarjejeniyar inshora din ta ƙunshi hakan.


4 Takardar yiwa abin hauwa rijista


Haƙiƙa takardar rijista na nuni ga hukuma cewa wanan abin hauwan fa an bi kafatanin ƙa’idar da duka ta shimfida kafin mallakar sa ko daura shi ga titi, domin haka duk ma’aika basu kama mai tuki da wanan laifi ba sai dai wani da bam.


5 Takardar shaidar mallaka


It takardar shaidar mallaka amfanin ta shi ne isar da tabbaci ko ingancin kasancewar abin hauwan na mai tuki ne, kuma hukumar VIO ke da hurumin bayar da ita. Rashin ta ka iya salwantar ma mutum abin abin hauwan sa dalilin rashin shaida.


6 Takardar lamincewa nauyin kaya da masu abin hauwa za su iya dauka


Ana mata laƙabi da (hackney permit) kuma ana mallakar ta yayin rijistar abin hauwan ne, domin ko ita ce zata zayyane iyakar kayan daya dace a dauka a mota a yayin tuki a manyan hanyoyin kasar nan, duk da ma ba ma’aikacin da ya damu da dubuwa. Garurruka kamar Ikko na tsanantawa domin mallakar wanan takarda. Wataƙila sauran jihohi kamar Kano ma su fara domin ceto titi daga mutuwar ba zata.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan