Wannan al’amari ya faru ne a yammacin jiya laraba, in da takaddama ta kaure tsakanin wani Mai mota da Mai babur din adaidata sahu, sakamakon Mai babur din ya gogar masa mota.
Bayan da takaddamar ta yi tsanani ne sai wani dan sandan da ke Gadi a bankin Union, daf da in da ake takaddamar ya fito a lokacin da yaga takaddamar ta yi tsamari, ya bukaci da su matsa gaba kasancewar ba’a tsayawa a bakin banki.
Nan take Mai motan ya shiga zai gyara motar daga bakin bankin, amma duk da haka sai wannan dan sandan ya daga bindiga ya harbeshi, take harsashi ya fasa glass din motar ya sameshi a wuya, a zatonshi wai mutumin guduwa zai yi.
Kakakin Yansandan jihar Kano SP Haruna Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin Inda yace tuni aka kama Dan sandan in da ake cigaba da bincike akan sa.
Ya kuma tabbatar da cewa an garzaya da mutumin asibitin malam Aminu Kano inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Madogara
Arewa radio.
