Home / Labarai / Yadda Ɗalibai Ke Ɗaukar Darasi A Mazaɓar Garo Da Ke Jihar Kano

Yadda Ɗalibai Ke Ɗaukar Darasi A Mazaɓar Garo Da Ke Jihar Kano

Ilimin Furamare na ƙara samun koma baya a wasu daga ƙananan hukumomin jihar Kano duk da kuɗaɗen da gwamnatoci ke warewa fannin na ilimi.

Ƙarancin kujerun zama da kayan aiki na koyo da koyarwa na ci gaba da kassara karatun ‘ya’yan talakawa a waɗannan ƙananan hukumomi.

Ƙauyen Alkalawa da ke mazaɓar Garo a cikin ƙaramar hukumar Kabo a jihar Kano, na fama da matsalar rashin ajujuwan makaranta a ƙauyen na su.

Matsalar rashin ajujuwan ta sanya al’ummar wannan ƙauye yin amfani da karan Masara da na Gero wajen yin rumfar da ƴaƴansu za su dauki darasi a ciki.

Sai dai kuma a cikin Satumbar bana ne gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta ƙaddamar da shirin ilimi kyauta a faɗin jihar Kano.

About Labarai24

Wannan Jarida ce ta shafin Intanet dake kawo muku labarai da rahotannin. har da Bidiyo da Audio.

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *