Rashin Ƙirƙirar Masarautu Shi Ya Fi Alheri A Kano – Sheikh Aminu Daurawa

355

Fitaccen malamin addinin Islama kuma tsohon kwamandan hisbah na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya buƙaci gwamnatin jihar Kano ta gudanar da ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a kafin yin gaban kanta wajen ƙirkirar sabbin masarautu a jihar.


A yayin zanta wa da sashen Hausa na RFI, Sheikh Daurawa ya ce, suna ganin rashin kirkirar sabbin masarautun shi ya fi alheri domin kauce wa wargaza kawunan al’umma.


Tuni Majalisar Dokokin Jihar ta amince da dokar kirkirar sabbin masarautunu bayan gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da kudirin dokar ga Majalisar.


Cikin gaggawa ‘yan Majalisar suka amince da wannan doka a ranar Alhamis duk da cewa babbar kotun jihar ta soke sabbin masarautun tare da dakatar da sarakunan da gwamnan ya nada.


Shugaban masu rinjaye a Majalisar dokokin, Labaran Abdul-Madari ya ce, manufar kirkirar sabbin masarautun, ita ce bunkasa ci gaba a fadin jihar, kuma a cewarsa, sun dauki matakin ne domin talakawa.


A shekarar da ta gabata ne, gwamna Ganduje ya kirkiro masarautun, matakin da ake kallo a matsayin yunkurin rage karsashin Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi wanda ake ganin ba sa jituwa saboda wasu dalilai na siyasa.


Sabbin masarautun sun hada na Bichi, karkashin Aminu Bayero. sai ta Rano, karkashin Tafida Abubakar-Ila da ta Karaye wadda aka bai wa Ibrahim Abubakar, sai kuma ta Gaya, karkashin Ibrahim Abdulkadir.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan