Hajia Rabi Saulawa Ta Zama Sabuwar Shugabar Jam’iyyar Matan Arewa

505

An zaɓi Hajiya Rabi Musa Saulawa a matsayin sabuwar shugabar Jam’iyyar Matan Arewa, in da ta yi nasara akan abokiyar karawarta Hajiya Aishatu Ismail.

Tun da farko an gudanar da zaɓen ne a yau lahadi a Otel 17 da ke Kaduna, in da Rabi Saulawa ta samu ƙuri’u 80 ya yin da tsohuwar ministar harkokin mata Hajia Aishatu Ismail ta samu ƙuri’u 79.

Da ta ke jawabi jim kaɗan da bayyana ta a matsayin wacce ta lashe zaɓen, Rabi Saulawa ta yi alƙawarin haɗa kan matan da su ke yankin arewacin ƙasar nan guri guda tare da ba su goyon baya a cikin al’amuransu.

An dai kafa Jam’iyyar Matan Arewa ne a cikin shekarar 1963 da nufin damawa da matan arewacin ƙasar nan a harkokin Ilimi da matsalolin haihuwa da kuma walwala da jin daɗin mata.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan