Masu naɗa sarki a Masarautar Kano sun sake kai karar Gwamna Abdullahi Ganduje da gwamnatin jihar da majalisar dokokin jihar a gaban kotu, abin da ke nuna da alama har yanzu da sauran rina a kaba a rikicin kafa sabbin masarautu a jihar.

Madakin Kano da Makaman Kano da Sarkin Dawaki Mai Tuta da kuma Sarkin Ban Kano, na neman kotun ta taka wa Gwamna Ganduje da gwamnatin jihar da majalisar dokoki.
Wadanda ake karar sun kuma hada da kwamishinan shari’a kuma babban mai shigar da kara na gwamnatin jihar daga daukan kowane irin mataki dangane da sabuwar dokar masarautun jihar.
Har wa yau, wadanda ake karar sun hada da sarakunan sabbin masaratun Bichi da Gaya da Karaye da kuma Rano, wadanda a baya kotu to soke nadin da gwamnatin jihar ta yi musu.
Masu nada sarkin na kuma bukatar kotun ta dakatar da bangaren gwamnati da majalisar jihar daga tattaunawa ko yin mahawara ko amincewa ko yin gyara ko yin wani abu a kan sabuwar dokar, har sai kotu ta yanke hukunci a kan karar da aka shigar a kan lamarin.
Masu shigar da karar na zargin gwamnan jihar da yin azarbabin sanar da cewa za ta ci gaba da daukar sarakunan da kotu ta soke matsayin halartattu, jim kadan bayan kotu ta soke sabuwar dokar da ta kafa masarautunsu a matsayin haramtacciya saboda rashin bin ka’idoji wurin zartar da ita.
Suna kuma zargin wadanda ake karar da yi wa umurnin kotu karan-tsaye, ta hanyar gabatar da sabuwar dokar kafa sabbin masarautu da bangaren gwamnatin ya gabatar wa majalisar dokokin jihar da kuma yin mahawara da zartar da dokar a majalisar, bayan kotu ta dakatar da su daga sabunta dokar da ta kafa masarautar mai dadadden tarihi.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai Gwamna Ganduje ya nada Sarki Muhammadu Sanusi a matsayin shugaban majalisar sarakunan jihar, bayan gwamnan ya rattaba hannu a kan sabuwar dokar masarautun jihar, mai cike da rudani.
Rahoton BBC Hausa