Kano Pillars Natajiran Gawon Shanu Akan Miliyan 25 Daga NFF

225

Watanni 4 kenan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars tana yin jiran gawon shanu dangane da kudin da hukumar kwallon kafa ta kasar nan zata biya ta na gasar Aiteo Cup da suka lashe.

Ko awatan daya gabata kungiyar kwallon kafan ta Kano Pillars ta koka dangane da kin biyan kudin inda har aka fitar da wani rahoto na kanzon kurege cewar anbiyasu ashe ba haka bane.

Jami’in yada labaran kungiyar kwallon kafan ta Masu Gida ne ya bayyanawa jaridar Labarai24 cewar har yanzu ba a biya kungiyar kudinta ba naira miliyan 25.

Kano Pillars dai sun lashe gasar karon farko a tarihi daci 4 da 3 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Shin ko yaushe wannan gawon da Kano Pillars suke ta jira zai fado?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan