Gwamnatin Kano tace Duk mai tuka babur mai kafa Uku da yake ganin Yafi karfin doka to Ya Jira zuwa lokacin da za a rufe yin rajistar masu Adaidaita Sahu, yaga yadda zasu kwashi Yan kallo da jami’an Karota matukar ya hau titin Gwamnati.
Shugaban hukumar karota Baffa Babba Dan Agundi, ya bayana hakan yayin taron manema Labarai da ya gudana Yau a shelkwatar karota dake Titin Kulob Road a nan Kano.
Dan Gundi, ya kara da cewar tsarin da Gwamnatin Kano ta Fito dashi ya zama wajibi don inganta harkokin tsaro da kuma sanin masu gudanar ta sana’ar Tuka Adaidaita Sahu a jihar Kano.
Baffa Babba Dan Agundi, ya kuma kara da cewa Gwamnati Bata yanke kaidar abunda za a karba daga gurin masu babura mai kafa uku ba saida ta zauna da shugabannin kungiyoyinsu wannda sunema suka yanke abunda za a karba daga garesu.
Sai dai kwamandan hukumar bai amsa tambaya daga manema labarai game da karancin fitowar jami’an na Karota, kamar yadda aka saba ganinsu ba a yau, yayinda ofishin Karotar Yakasance a zagaye da Jami’an Yansanda don tabbatar da doka da Orda.
Rahoton Dala FM Kano
