Barcelona Sun Zubar da Maki Gab da El-Clasico

151

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona wadda take jan ragamar teburin gasar Laliga ta kasar Andalos ta zubar da maki biyu gab da wasan El-Clasico.
Barcelona sun zubar da maki biyu ne awasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Real Sociedad ayau da yamma.
Yanzu dai aranar Laraba Barcelona zasu fafata wasa da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wasan da aka yiwa lakabi da El-Clasico.
Amma kafin wasan na El-Clasico agobe Lahadi Real Madrid zatayi tattaki zuwa gidan Valencia.
Shin ko Real Madrid zasu iya lashe Valencia awasan gobe domin hawa teburin Laliga? Kokuwa suma zasu gaza kamar yadda Barcelona suka kasa samun maki 3 akan Real Sociedad?

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan