Tarihin Sarkin Bai Mukhtar Adnan: Hakimin Da Ya Yi Adabo Da Hakimcin Sa Bayan Da Ya Shafe Shekaru 64 Yana Yi

322

An haifeshi a shekarar 1926 a garin Ɗambatta ya kuma fara karatun sa na elementari a makarantar Dambatta a cikin shekarar 1935 daga bisani kuma ya shiga makarantar midle ta Kano, bayan ya kammala Midle sai ya zarce zuwa makarantar harkokin mulki ta jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

A cikin shekarar 1944 Sarkin Bai ya fara aikin gwamnati da makamin malamin hakimi a garin Ɓabura, daga baya ya dawo Dambatta .

Bayan wasu shekaru da ya kwashe yana aiki a matsayin Malamin Hakimi, sai kuma ya dawo N. A in da ya riƙe akanta a sashen kudi, daga nan likkafa ta cigaba in da har ya kai matsayin babban malami a N. A.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I shi ne ya naɗa Alhaji Mukhtar Adnan Sarkin Bai Hakimin Ɗambatta a cikin shekarar 1954, abin da ya sa ya fi kowane Hakimi dadewa a masarsutar Kano, domin kuwa ya shafe shekara 64 yana Hakimci.

A cikin shekarar ya zama dan majalisa mai nadin Sarkin Kano inda bayan shekaru 9 suka nada Marigayi Sarkin Kano Dakta. Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano a cikin shekarar 1963.

Sarkin Bai, shi ne shugaban kabilar Dambazawa, wadanda tarihi ya nuna sun taimakawa Shehu Usmanu wurin yake-yaken jihadin da aka dauki shekaru ana fafatawa.

Tsohon gwamnan jihar Kano marigayi Audu Bako ya naɗa shi kwamishinan ilimi na farko a jihar Kano

A ranar Asabar 14 ga watan Disambar Shekarar 2019, Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero ya tumbuƙe rawaninsa sakamakon rashin yi masa mubaya’a

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan