Home / Labarai / Za Mu Amince Da Buƙatar Buhari Ta Ciyo Bashin Dala Biliyan $30- Sanata Lawan

Za Mu Amince Da Buƙatar Buhari Ta Ciyo Bashin Dala Biliyan $30- Sanata Lawan

A ranar Litinin ne Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmad Lawan ya ce Majalisar Dokoki ta Ƙasa za ta amince da buƙatar ciyo bashin dala biliyan $29.96 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar mata.

Sanata Lawan, wanda ya bada tabbacin yayinda yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja, ya ce amma Majalisar Dattijai za ta tabbatar an kashe bashin na dala biliyan $30 bisa aikace-aikacen da aka buƙace shi.

“Za mu tabbatar da cewa duk wani silai da aka ranta an yi wani aiki da shi”, in ji Sanata Lawan.

About Hassan Hamza

Check Also

Wasiyyar da marigayi tsohon shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua ya barwa ƴan siyasar Najeriya

A yau Laraba 5 ga watan Mayun shekarar 2021 tsohon shugaban Najeriya Malam Umaru Musa …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *