Jami’ar Abuja Ta Kori Malamai Guda Biyu Akan Zargin Fasiƙanci

201

Bayanai sun nuna cewa hukumar gudanarwar Jami’ar ce ta amince da korar malaman biyu bayan nazari kan rahoton da kwamitin da ta kafa na mutun takwas ya fitar.

Jami’in hulda da jama’a na jami’ar Dakta Habib Yakoob, ya ce an sallami Farfesa Adeniji Adebayo na sashen koyar da aikin gona da Farfesa Agaptus Chibuzo Orji na sashen koyar da kimiyar muhalli.

Manema labarai sun yi kokarin jin ta bakin daya daga cikin malaman Farfesa Adeniji Adebayo amma bai amsa waya ba, bai kuma amsa gajeren sakon da a ka aika masa ba.

Idan za’a iya tunawa dai a cikin watan Oktoba ne sashen BBC da ke binciken kwakwaf na (Africa Eye) ya fallasa yadda wasu malaman jami’ar ke neman ci da gumin dalibansu mata, ta hanyar lalata da su don ba su makin jarrabawa a wasu jami’o’in ƙasar nan da Ghana.

A kan haka ne ma hukumomi a ƙasar nan ke yunkurin fito da wata doka da za ta hukunta masu irin wadannan laifuka.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan