Wannan shi ne karon farko da sarakunan jihar Kano guda biyar suka fara haduwa da juna tun bayan kafa sabbin sarakuna guda hudu a jihar.



Sarki Muhammadu Sanusi II ya isa wurin ne taron bayan sarakunan Bichi da Rano da Gaya da kuma Karaye, wadanda hakimai ne a masarautar Kano, kafin gwamnatin jihar ta nada su sarakuna a sabbin masarautun a ‘yan watannin baya.
Sai dai sabbin sarakunan ba su gaisa da Sarki Sanuni ko sun yi magana da shi ba ko nuna sanayya har bayan taron.
Hakan ta sa aka yi mamaki, duba da dadaddiyar sanayyar da ke tsakaninsu da kasancewar dukkansu ‘yan majalisar masarautun jihar kuma manyan baki a wurin taron.
Yayin da Sanusi ya iske sauran sarakunan zaune a kusa da juna, tawagarsa ta iske wani basarake daga babban birnin Tarayya zaune a kujerar Sarki Sanusi a wurin.
Sakamakon haka ne aka ware wa Sarkin wani wurin zama, abin da wasu ke gani a matsayin kaskantar da shugaban majalisar sarakunan jihar.
Bayan zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari taron, an sauya wa Sarki Sanusi wurin zama inda ya koma kusa sa shugaban kasar a teburin da aka ware wa manyan bakin alfarma.
A karshen taron Shugaban kasar ya gaisa da Sarkin Kano Sanusi amma sauran sarakunan ba su samu damar yin hakan ba, kasancewar Sarki Sanusi ne kadai a cikinsu ya ke sahun farko na manyan baki da ke kusa da shugaban kasar.
[…] Muƙalar Da Ta GabataShugaban Ƙasa Buhari Bai Gaisa Da Sababbin Sarakunan Kano Ba […]