Ƙungiyoyi Sama Da 180 Sun Nuna Goyon Baya Ga Sarki Sanusi

407

Wata gamayyar ƙungiyoyin fararen hula 183 da wasu ƙungiyoyin al’umma a ƙarƙashin tutar Inuwar Ƙungiyoyin Fararen Hula na Kano, KCSF, sun nesanta kansu daga buƙatar tsige Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II da wasu ƙungiyoyi da ba a san su ba suka gabatar ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Majiyarmu ta ruwaito cewa Gwamna Ganduje, ta hanyar Sakataren Yaɗa Labaransa, Abba Anwar, a ranar Alhamis ya tabbatar da karɓar wata wasiƙa daga ‘ƙungiyoyin fararen hula’, inda suka yi kira a gare shi da ya tsige Sarkin bisa zargin rashin biyayya ga gwamnati.

“Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya karɓi wata wasiƙa daga gamayyar ƙungiyoyin fararen hula 35 inda suke roƙon sa, don kare martabar doka, da kuma dama da masu zaɓe na Kano suka ba shi, a matsayin wata magana ta gaggawa, ya fara shirye-shiryen tsige Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II”, in ji sanarwar.

Mista Anwar ya ce wani Ibrahim Ali, shi ne ya sanya hannu a kan wasiƙar a madadin ƙungiyoyin fararen hular 35 da ba a san sunansu ba.

“Kwamared Ibrahim Ali, Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin, shi ya sanya hannu a kan wasiƙar, wadda ta ci gaba da cewa, ba da daɗewa ba, dokar da ta soke dukkan Dokokin Majalisar Masarautun Kano da ake aiki da su a halin yanzu, sannan Dokar Masarautun Kano ta 2019 ta ƙarfafe su, sai kuma ga shi masu naɗa sarki guda biyar daga ɗaya daga cikin masarautun da dokar ta ƙirƙira suna ƙalubalantar ta”, ya faɗi haka a cikin wata sanarwa.

Amma, ranar Juma’a, KCSF, a cikin wata sanarwa da Ibrahim Wayya Rayya, Mai Magana da Yawunta ya fitar, ta nesanta kanta daga kiran tsige Sarkin, inda suka yi kira a kama Mista Ali, mutumin da ya sa hannu a wasiƙar da aka aika wa Gwamna Ganduje.

“Abin damuwa ne yadda wasu ƙungiyoyi masu ra’ayin siyasa waɗanda ba a san su ba, za su yi iƙirarin cewa suna wakiltar wasu ƙungiyoyin fararen hula a Kano, waɗanda ake zargin sun yi kira ga Gwamna da ya tsige Sarkin Kano, Mallam Muhammad Sanusi II.

“Da a ce wannan gungun ƙungiyoyi da gaske suke suna wakiltar ƙungiyoyin fararen hula ne, da sun ƙarar da ƙarfinsu a wajen haɓaka zaman lafiya, haɓaka shugabanci na gari, ci gaban zamantakewa da na tattalin arziƙi, haɓaka walwala da jin daɗin al’ummar Kano, su kuma tabbatar da zaman lumana a jiharmu, amma ba abinda suka yi yanzu ba.

“A bisa wannan, muke son tona asiri kuma mu nesanta Inuwar Ƙungiyoyin Fararen Hula na Kano daga matsayin wannan ƙungiya mara rijista, wadda ba a santa ba, kuma ta bogi, waɗanda daga abinda sanarwarsu ta ƙunsa sun nuna ba su da hikima, ba sa son zamna lafiya, kuma ba su da alƙibla a siyasa”, a cewar sanarwar.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan