Attajiran Ƙasar Nan Na Safarar Kuɗaɗensu Zuwa Ƙasashen Turai

469

Ƙasar nan na daya daga cikin kasashen da talauci ya zama ruwan dare a nahiyar Afirka, attajirai na safarar kudadensu zuwa wuraren da ake kira “tax haven” wato wuraren da ba a biyan haraji.


A Abu Dhabi, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa, an gudanar da Taron Majalisar Dinkin Duniya na 8 kan yaki da cin hanci da rashawa inda aka tattauna kan kin biyan haraji da safarar kudade.


Ministan shari’a na ƙasa Abubakar Malami, a jawabin da ya yi a taron ya ce kudin da masu arzikin kasar suka kai “tax haven” ya wuce dala biliyan 400.


Malami ya bayyana cewa kamfanonin kasa da kasa da abokkan aikata laifukansu na kasashen waje sun sace kudaden kasar nan tare da safararsu kuma gwamnati ta dauki tsauraran matakai domin dakile hakan.


Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya karbi mulki a shekarar 2015, ya fara yaki da cin hanci da rashawa a kowanne bangare.


Duk da cewa kasar nan tana samun kudaden shiga daga arzikinta na karkashin kasa kamar mai da iskar gas amma rashawa da cin hanci suna daga cikin abubuwanda ke haifar da matsaloli a fadin ƙasar nan.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan