Tarihin Mai Martaba Sarkin Ƙaraye Alh (Dr) Ibrahim Abubakar Il

  936

  An haifi mai martaba Sarkin Ƙaraye Alhaji (Dr) Ibrahim Abubakar II a garin Ƙaraye da ke jihar Kano, a ranar 7 ga watan Yulin Shekarar 1954. Ya fara karatun allo a gurin malaminsa mai suna Abdu Goga, daga nan ya wuce makarantar Furamare da ke garin Ƙaraye wato Ƙaraye Central Primary School.

  Bayan kammala karatun Furamamre ya wuce babbar sakandiren gwamnati da ke Ɗambatta. Bayan kammala karatun sakandire ya samu nasarar shiga kwalejin horon malamai da ke jihar Kano inda ya samu satifiket akan keken rubutu.

  Mai martaba Sarkin Ƙaraye ya samu halartar kwalejin kimiyya da fasaha da ke Kaduna inda ya samu ƙwarewa tare da samun wani satifiket din.

  Bayan kammala karatunsa a kwalejin kimiyya da fasaha da ke Kaduna, ya wuce jami’ar Lincoln da ta ke jihar Missouri a ƙasar Amurka, inda ya karanta tsimi da tanadi wato ECONOMICS. Ya kuma samu digirinsa na biyu akan harkokin kasuwanci daga Jami’ar Bayero da ke Kano.

  Mai martaba Sarkin Ƙaraye ya fara aiki a ma’aikatar ciniki da masana’antu da kasuwanci ta jihar Kano. A cikin shekarar 1979 zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rmi ya naɗa shi a matsayin sakataren sa na musamman.

  A cikin shekarar 1988 ya bar aikin gwamnati inda ya koma aiki da kamfanin motoci na Steer da ke jihar Bauchi, sannan kuma ya yi aiki da kamfanin wutar lantarki na NEPA, a matsayin manajan kasuwanci.

  A shekarar 1996 gwamnan soji Dominic Obukadata Oneya ya naɗa shi a matsayin kwamishinan ciniki da masana’antu na jihar Kano.

  A ranar 3 ga watan Aprilu na shekarar 1998 marigayi mai martaba Sarkin Kano Alhaji Dakta Ado Bayero ya naɗashi Sarkin Ƙaraye hakimin gundumar Ƙaraye.

  Mai martaba Sarkin Ƙaraye ya samu digirin girmamawa akan harkokin kasuwanci daga Jami’ar Albert da ke ƙasar Kanada a shekarar 2004.

  Mai martaba Sarkin Ƙaraye yana da matan aure guda 3 da ƴaƴa da dama.

  A ranar 10 ga watan Mayun shekarar 2019 gwamnatin jihar Kano ƙarkashin shugabancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta tabbatar da Sarkin Ƙaraye Alh. (Dr) Ibrahim Abubakar Il a matsayin Sarki Mai daraja ta daya tare da Sarakunan Bichi, Rano, da Gaya.

  Turawa Abokai

  1 Sako

  RUBUTA AMSA

  Rubuta ra'ayinka
  Rubuta Sunanka a nan