An Fitar Da Gwarzon Shekarar Gasar Karatun Ƙur’anin Na Kano Na 2019

363

A ranar Lahadi ne aka fitar da Gwarzon Shekarar Musabaƙar Karatun Ƙur’ani na 2019 wadda Gidan Talabijin na Muhammadu Abubakar Rimi, ARTV, dake Hotoro, ƙaramar hukumar Tarauni a jihar Kano ya shirya.

Labarai24 ta ruwaito cewa an gudanar da Gasar Karatun Ƙur’anin ne ƙarƙashin jagorancin Hajiya Sa’a Ibrahim, Shugabar Gidan na ARTV.

Majiyarmu ta ce an fara Gasar Karatun Ƙur’anin ne tun a watan Janairun 2019, inda aka gudanar da ita wata-wata.

Majiyar ta ƙara da cewa an gudanar da Gasar Karatun Ƙur’anin ne daga matakin ƙaramar hukuma har zuwa matakin shiyya.

Bayan kammala gasar a matakin ƙaramar hukuma da shiyya, sai aka fito da ‘yan takara guda tara, waɗanda suka yi ƙara fafatawa, inda guda huɗu suka samu damar shiga takarar fitar da Gwarzon Shekarar na 2019 a matakin Izifi 20 da aka gudanar ranar Lahadi.

Da yake bayyana sakamakon takarar, Shugaban Alƙalan Musabaƙar, Malam Abubakar Chiranci ya bayyana Ahmad Muhammad Harun a matsayin wanda ya zo na ɗaya da maki 95 da rabi cikin ɗari.

A jawabinsa bayan da ya yi nasara a mataki na ɗaya, Mista Muhammad ya yi godiya ga Allah bisa wannan nasara da ya ba shi.

Ya kuma gode wa malamai da iyaye da suka jajirce ba tare da gajiyawa ba don ganin ya yi ruƙo da Ƙur’ani.

Ya yi kira ga al’umma da su faɗaka su gane cewa babu littafi kamar Ƙur’ani, su kuma gane cewa shi ne littafin da idan aka riƙe shi, zai kai mutum tudun-mun-tsira duniya da lahira.

“Ina godiya ga Allah subhanahu wata’ala bisa wannan nasara da ya ba ni, ba dabarata ba ce kuma ba iyawata ba ce. Kawai sai dai illa iyaka, taimkon da Allah subhanahu wata’ala Ya ba ni, Ya ƙaddara min zan samu wannan mataki na ɗaya”, in ji Mista Harun.

Mista Harun ya samu kyautar sabon babur, N20,000, bargo, yadi, atamfa da sauran kyaututtuka.

Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Kabo, wanda ya samu wakilcin Sanatan Kano ta Kudu, Barau Jibrin-Maliya ya yi alƙawarin ba na ɗaya sabon babur, ya yi wa na biyu alƙawarin kyautar N100,000, na uku, N70,000, inda ya yi wa na huɗu alƙawarin N50,000.

Sauran manyan baƙin da suka halarci taron sun haɗa da Shugabar Gidan Talabijin na ARTV, Hajiya Sa’a Ibrahim, da Sanatan Kano ta Tsakiya, Barau Jibrin-Maliya.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan