Gasar Firimiyar Ingila Ta Tara Mnyan Masu Horas Wa

153

Tabbas zuwan Anceloti kungiyar kwallon kafa ta Everton ya karawa kungiyar kwarjini duba da yadda ko a duniya ake lissafin manyan masu horas wa sai an saka Carlo Anceloti duba da irin gudun mawar daya bayar a duniyar kwallon kafa amatsayinsa na mai horas wa.

Yanzu idan akayi duba a kasar ta Ingila akan manyan masu horas wa akwai Jose Mourinho na Tottenham da Pep Guardiola na Manchester City da Jurgen Klopp da kuma Carlo Anceloti.

Wadannan masu horas wa manyane a duniya inda kowannensu ya lashe gasar league sannan ya lashe gasar zakarun nahiyar turai.

Domin dukkaninsu su 4 sun lashe gasar league har guda 22 sannan sun lashe gasar zakarun nahiyar turai guda 8.

Sannan yanzu batun da akeyi gasu dukkaninsu sun taru a gasa guda 1 kuma zasu dinga haduwa atsakaninsu aduk shekara.

Shin ko yaya kasar Ingila zata kasance wajen nuna bajintar masu horas wa nan da wasu shekaru?

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan