Ramuwar Gayya Ce Ta Sanya Buhari Ya Garƙame Dasuƙi – Sule Lamido

1595

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya ce sakin Sambo Dasuki da Ministan shari’a ya sa aka yi, ya nuna cewa tun farko ba zargin satar kudi ta sa aka kama shi ba.

Sule Lamido ya bayyana cewa garkame tsohon mai bada shawara akan harkar tsaron bai da wata alaka da badakalar kudin makamai sama da Dala biliyan biyu.
‘Dan siyasar ya fadawa ‘Yan jarida a wayar tarho cewa tsare Sambo Dasuki da aka yi, ya na da nasaba ne da sabanin da ke tsakaninsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
“Babu abin da ya hada (kama shi da aka yi) da rashin gaskiya. An gayyaci Dasuki an yi masa tambayoyi wanda bayan nan aka gurfanar da shi a gaban kuliya da zargin laifi.”
“Cigaba da tsare shi na kwana guda bayan kotu ta bada belinsa ya sabawa doka, bai dace ba, kuma bai kamata gwamnati ta yi wannnan aikin duhun kai ba. Ba batun kudi bane.”

Akwai hukuncin da Alkali mai shari’a Binta Nyako, ta yi na cewa bai halatta a kama mutum a rufe a kan umarnin wani babban jami’in gwamnati ba, har ma shugaban kasa.

“Bai yi laifin komai ba, idan ana maganar rashin gaskiya ko bacewar kudi. (Dasuki) ya bi umarnin da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ba shi ne.” Inji Sule Lamido.

Tsohon Ministan wajen ya ce: “Surutun Mutane ya sa gwamnati ta yi abin da ya dace. Dama can Buhari ya na da tarihin sabawa doka. Daure Dasuki kadan daga cikin aikin sa ne.”

Sule Lamido ya nuna cewa Najeriya ta shiga matsala a irin wannan mulki mai-ci, ganin yadda Buhari ya taba fitowa karara ya ce ya raina tsarin tafiyar mulkin fafar hula.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan