Home / Featured / Shekaru 70 Na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje: Me Ka Sani Game Da Shi?

Shekaru 70 Na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje: Me Ka Sani Game Da Shi?

An haifi Dakta Abdullahi Umar Ganduje Ranar 25 ga watan Disambar shekara ta 1949.

Maihifinsa Alhaji Umar Shi’aibu Shi ne; Dagacin kauyen Ganduje, dake karamar Hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano.

Ya fara karatunsa na zamani na Makarantar Firamare a Shekarar 1956 zuwa 1963.
Dakta Ganduje ya halarci Shahararriyar babbar Makarantar Sakandiren Gwamnati ta Birnin Kudu a Shekarar 1964 zuwa 1968.

Ya mallaki Shaidar Shahadar Malanta ta kasa(NCE), A Babbar Kwalejin horas da Malamai ta Kano (Advance Teachers’ College Kano) A tskankanin shekarar 1969 zuwa 1972.
Har-ila-yau Dakta. Ganduje ya sake halartar Jami’ar Ahmadu Bello (ABU Zaria) don samun mallakar Shaidar Digiri na daya A fannin ilimi da kimiyya (Bachelor degree in Science Education) daga shekarar 1972 zuwa 1975. Dr. Ganduje ya samu shaidar digirinsa na biyu A fannin Ilimi da Kimiyyar halaye da dabi’un Dan Adama (Masters degree in Applied Educational Psychology) A Jami’ar Bayero, Kano A Shekarar 1979. Sannan kuma ya sake koma wa Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya daga Shekarar 1984 zuwa 1985 don sake wani sabon Digirin na biyu har-ila-yau a fannin Al’amuran Gudanarwa (Masters in Public Administration).

Ya kuma halarci Jami’ar Ibadan dake Kudu-maso-Kudancin Nijeriya don samun Shahadar Digirin Digir-gir, wato Digiri na uku (PhD) a fannin Al’amuran Gudanarwa (Public Administration) A Shekarar 1989 zuwa 1993.

About Buhari Abba Rano

Buhari Abba Rano is a Skilled and News-Oriented Journalist With a Vision to Provide Fair, Fresh, Prompt and Truthful News.

Check Also

Kanywood: Lalacewar Fina- Finai, Laifin Waye?

“Bala Ana’s babinlata kunyi kuskuren barin Jahilai su jagoranci wasan kwaikwaiyo a camfanin kanny wood …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *