Jami’ar Bayero Da Ke Kano Ta Fara Samar Da Shinkafa

281

Hotunan buhun-hunan shinkafa mai ɗauke da tambarin jami’ar da ke Kano, wanda sashen tattalin arziki da albarkatun noma na jami’ar su ka samar ya cika kafafen sada zumunta na zamani.

Tun da farko dai hotunan buhun-hunan shinkafar sun fara yaɗuwa a shafukan fasebuk da sauran kafafen yaɗa labarai na zamani a yau larabar 26 ga watan Disambar shekarar 2019.

Jaridar Labarai24 ta ci karo da sanarwar tabbacin shinkafar daga jami’ar ta Bayero ta ke, bayan da Jami’ar wallafa hakan a shafinta na fasebuk.

Sai dai abin tambayar shi ne gwaji ne aka fara ko kuma jami’ar ta gama shiryawa wajen samar da wadatacciyar shinkafa ga al’ummar jihar Kano?

Tun da aka rufe iyakokin ƙasar nan da gwamnatin tarayya ta yi ƙarƙashin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ake ta samun sababbin masana’antun shinkafa, wanda a baya al’ummar ƙasar nan ta dogara ne kacokam akan shinkafa ƴar waje.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan