Tabbas Lingard Ya Ajiye Tarihi a 2019 a Manchester

261

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta ta Manchester United kuma dan asalin kasar Ingila wato Jese Lingard ya ajiye tarihi a shekarar da ake bankwana da ita ta 2019.

Saidai shi wannan dan wasa za a iya cewa tarihin daya ajiye ya bambamta da sauran tarihin da sauran ‘yan wasa suke ajiyewa tunda mummunan tarihi ya kafa.

Inda ayanzu haka dan wasan ya zai karkare shekarar nan ta 2019 batare da yaci kwallo a kungiyar ba kuma bai taimaka anci kwallo ba.

Rabon da Lingard yayi kokarin cin kwallo ko ya taimaka aci kwallo tun awatan Disamba na 2018.

Amma kuma wani abin mamaki shine kusan ko yaushe ana saka wannan dan wasa awasanni da dama tunda ba zaman dumama benci yakeyi ba.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan