Hisba Ta Kano Ta Cafke Ma’aurata Sakamakon Yin Aure Ba Da Izinin Iyayensu Ba

416

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta cafke wani saurayi da budurwarsa bisa zargin su da yin aure ba tare da sanin iyayensu ba.

An ce matasan ma’auratan, waɗanda ba a bayyana sunayensu ba, sun yanke shawarar yin auren ne bayan da suka ga wani mutum da matarsa suna rungumar juna a bainar jama’a, a lokacin da su kuma sun zo wucewa.

An gano cewa saurayin da budurwar, dukkaninsu mazauna yankin Kurna dake birnin Kano, sai suka yi aure a kan sadaki na N20,000, suka kuma buƙaci abokansu su zama waliyyansu.

Mataimakin Kwamandan Hisba, Malam Shehu Tasi’u Ishaq ya faɗa wa gidan rediyon Dala FM cewa abokan ma’auratan ne suka ɗaura auren bayan da angon ya biya N2,000, inda ita kuma amaryar ta ranta masa N18,000 domin ya cika N20,000 kamar yadda suka yi yarjejeniya.

Mista Ishaq ya ce wata uku da yin auren, angon ya ci gaba da saduwa da ‘matar’ tasa, abinda ya haifar da samun juna biyu.

Ya ƙara da cewa koda yake dai auren ɓatacce ne saboda ba a nemi izinin mahaifin yarinyar ba, amma ba za a ce mutumin da budurwa tasa sun aikata zina ba, kuma yaran da yake cikin nata ma ba za a ce masa shege ba.

Jami’in na Hisba ya kuma yi kira ga ma’aurata da su ƙaurace wa rungumar juna a bainar jama’a, yana mai cewa irin haka yana haifar da rashin ɗa’a a cikin al’umma.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan