Mashahuran Mutanen Da Jihar Kano Ta Rasa A Shekarar 2019

421

A shekara ta 2019, jihar Kano ta rasa mashahuran mutane waɗanda suka ba jihar, ƙasa da al’ummominsu daban-daban gudunmawa. Ga wasu mashahuran mutanen da suka rasu a ƙasa:

Umar Sa’idu Tudunwada, tsohon Manajan Darkatan Gidan Rediyon Kano

A ranar Lahadi, 30 ga watan Yuni, tsohon Manajan Darkatan Gidan Rediyon Kano, Umar Sa’idu Tudunwada ya rasu a wani haɗarin mota a garin Kura dake kan Titin Zariya zuwa Kano.

Har lokacin rasuwarsa, shi ne Mataiamkin Shugaban Ƙungiyar Masu Tace Labarai ta Ƙasa, NGE.

Lokacin da yake a raye, ya yi aiki da Hukumar Kula da Gidajen Talabijin ta Ƙasa, NTA, da kuma Gidan Talabijin na Gwamnatin jihar Kano, CTV 67, kafin ya ajiye aiki bisa raɗin kansa, inda ya koma Gidan Rediyon DW Hausa.

Marigayi Mista Tudunwada ya kuma yi aiki da Muryar Amurka (Sashin Hausa, Freedom Radio da Dandal Kura, Maiduguri, jihar Borno.

Ya kuma zama Mai Bada Shawara na Musamman Kan Kafafen Watsa Labarai ga tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, Ibrahim Shekarau da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Alhaji Shehu Azare, ɗan kasuwa

A ranar 8 ga Janairu, 2019, jihar Kano ta rasa wani mashahurin ɗan kasuwa, Alhaji Shehu Muhammad Azare, mazaunin unguwar Fage, a ƙaramar hukumar Fage.

An haifi marigayi Mista Azare ne a shekarar 1927 a ƙauyen Galdimari dake karamar hukumar Giade, a jihar Bauchi.

Ya zo Kano a 1941, sannan ya zauna a Fage, inda ya auri matarsa ta farko.

Ya bar mata biyu, ‘ya’ya 21, jikoki 50 da tattaɓa kunne 33.

Alhaji Idris Abubakar

A ranar 18 ga watan Yuli, shahararren ɗan kasuwa a Kano kuma mamaallakin Mudatex Mudassir and Brothers, Alhaji Mudassir Idris Abubakar ya rasa mahaifinsa, Alhaji Idris Abubakar.

Marigayi Mista Abubakar ya rasu ne a Indiya, inda ya je don neman magani.

Alhaji Shehu Ringim

Gogaggen masanin aikin gwamnati, Alhaji Shehu Ringim, mazaunin unguwar Ƙwalli ya rasu ranar Alhamis, 17 ga Oktoba, yana da shekara 89.

Babban Limamin Kano, Farfesa Muhammad Sani Zahradden, shi ya jagoranci yi masa jana’iza a Ƙofar Kudu dake Fadar Sarkin Kano.

Ya bar mace ɗaya da ‘ya’a shida.

Marigayi Mista Ringim ya taɓa zama Kwamishinan Hukumar Zaɓe daga 1976-1979, kuma ya taɓa zama Babban Kwamishina a Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa daga 1981-1984.

Ya kuma yi aiki a matsayin mamba na Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen Majalisar Dokokin Jihar Kano da kuma mamba na Kotun Sauraron Ƙorafe-Ƙorafen Zaɓen Majalisar Dattijai da Majalisar Wakilai a jihar Delta, a 1992.

Alha Salisu Buhari

Alhaji Salisu Buhari, mahaifin tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Alhaji Ibrahim Salisu Buhari, ya rasu ranar Litinin, 1 ga Afrilu.

Marigayin, hamshaƙin ɗan kasuwa ya rasu a wani asibiti dake Misra, yana da shekara 83 bayan an yi masa wani aiki.

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, shi ya jagoranci jana’izar Mista Buhari, bisa rakiyar Babban Limamin Kano, Farfasa Muhammad Sani Zahraddeen, Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ‘yan Majalisar Masarautar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Mataimakisa, Nasiru Yusuf Gawuna

Mista Buhari ya taɓa zama Shugaban Kwamitin Dattawan Jam’iyyar APC, Reshen Jihar Kano da kuma Kwamitin Wayar da kai na ƙaramar hukumar Nasarawa.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan