An Hana Mu Ganin Ganduje Don Yin Sulhu Tsakaninsa Da Sarki Sanusi -Farfasa Abdullahi

1281

Farfesa Ango Abdullahi, Shugaban Ƙungiyar Dattawan Arewa, NEF, wanda ke jagorantar Kwamitin Sulhu da zai sasanta rikicin siyasa dake ci gaba da ruruwa tsakanin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya nuna rashin jin daɗi bisa yadda aka hana kwamitinsa ganawa da Gwamna Ganduje gaba da gaba.

Idan dai ba a manta ba, a watan Mayu na wannan shekarar ne Gwamna Ganduje ya ƙirƙiri sabbin masarautu huɗu a Bichi, Rano, Ƙaraye da Gaya, wani yunƙuri da ake yi wa kallon zai rage tasirin Sarki Sanusi, wanda Gwamna Ganduje ke zargi da goyon bayan jam’iyyar adawa ta PDP a jihar.

Mista Abdullahi, wanda ya yi wannan magana a wata tattaunawa da Vision FM, Kano, ya ce wasu mutane daga bayan fage sun umarci Gwamna Ganduje da ya yi watsi da buƙatar NEF ɗin ta son ganawa da shi gaba da gaba don ji daga gare shi, amma dai sun iya ganawa da Sarki Sanusi.

Ya kuma bayyana cewa wasu mutanen kuma, sun gaggauta sanar da sunan Abdulsalami Abubakar, tsohon Shugaban Mulkin Soja a matsayin shugaban wani kwamitin da shi ma zai yi aiki irin na kwamitinsu, kawai don dakusar da ƙoƙarin na NEF.

Ya bayyana cewa ba a tuntuɓi Mista Abdulsalam ba kafin a ba shi muƙamin, kawai sai dai ya ji sunansa a rediyo cewa shi ne shugaban kwamitin, kwamitin da aka ce yana da goyon bayan Gwamnatin Tarayya.

Ya ce kafa kwamitin da Mista Abdulsalami ke jagoranta wani mataki ne da waɗanda ke son nuna tasirinsu suka ɗauka rana tsaka, bayan da suka lura cewa NEF ta yi nisa wajen warware rikicin a Kano.

“Rikicin Kano ba shi da wani dalili, wani makircin siyasa ne kawai daga wasu mutane masu tunanin cewa su ne shugabanni, waɗanda suka bayyana rana tsaka, ba su damu da mutanen da ke sha wahala ba, kuma suna son rusa gidan tarihi da ya haura shekara 500 zuwa 1,000”, in ji Mista Abdullahi.

“Ni da kaina na tuntuɓi Janar Abdulsalami Abubakar, kuma ya faɗa min cewa kawai sai dai ya ji sunansa a rediyo”, ya ƙara da haka.

Mista Abdullahi ya ce sun zo Kano ne don su samu bayanai daga tushe game da rikicin, kuma “sun iya yin wani abu”.

Ya kuma zargi wasu ‘yan jarida da ƙoƙarin kare matakin da gwamnan ya ɗauka na ƙin ganawa da su gaba da gaba lokacin da suka shirya ganawar da shi, yana mai lura da cewa jajirtattun shugabanni ne kaɗai za su iya canza abubuwa a Najeriya.

Tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, ABU, Mista Abdullahi ya kuma ja kunnen shugabanni bisa muhimmancin Kano a Yankin Arewa, yana mai cewa ita ce kaɗai jihar da dukkan Yankin Arewa ke girmamawa.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan