Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS, ta magantu game da abinda ta bayyana a matsayin “yawaitar zarge-zarge” da wani yanki na kafafen yaɗa labarai ke yi mata cewa tana ci gaba tsare wasu ‘yan Najeriya ba bisa ka’ida ba.
Majiyarmu ta ruwaito cewa an yi ta zargin DSS da hannu a ɓatan Abubakar Idris, da aka fi sani da Dadiyata, wanda ya ɓata a jihar Kaduna da Agba Jalingo wanda ya ɓata a jihar Cross Rivers.
Sai dai a wata sanarwa da DSS ta fitar ranar Talata, Jami’anta na Huɗɗa da Jama’a, Peter Afunaya ya nesanta Hukumar da tsare Mista Dadiyata da Mista Jalingo, yana mai cewa : “Waɗannan zarge-zarge ba komai ba ne face tsagwaron ƙarya, kuma sai dai a bar su yadda suke kawai”.
“An jawo hankalin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS bisa yawaitar zarge-zarge da wani yanki na kafafen watsa labarai musamman jaridun Punch da Daily Trust cewa Hukumar na ci gaba da tsare wasu ‘yan Najeriya ba bisa ka’ida ba.
“Waɗanda aka kama sunayensu a keɓance su ne Abubakar IDRIS (da aka fi sani da Dadiyata) da Agba JALINGO, waɗanda aka ce Hukumar ta kama su a jihohin Kaduna da Cross Rivers.
“Wani zargin da ya bazu shi ne na Jaridar Punch bugun 6 da 29 ga Disamba, 2019, dake cewa Hukumar na tsare da mutane da take zargi da aikata laifuka fiye da 50, a wani yanayi mummuna, kuma “tana azabtar da su lokaci bayan lokaci”.
“Waɗannan zarge-zarge, ba komai ba ne face ƙarya tsagwaronta, kuma za a bar su ne yadda suke- zarge-zarge na karya da ake yaɗawa da gangan don yi wa Hukumar ƙafar angulu, kuma a zubar mata da mutunci a bainar jama’a.
“Cewa wasu mutane ɗauke da makamai sun ɗauki IDRIS daga gidansa sun tafi da shi ba ya nufin cewa waɗancan mutane ma’aikatan DSS ne. Ya kamata a ce Daily Trust da PUNCH sun gudanar da bincikensu yadda ya dace kafin su zargi Hukumar da wani abu da ba ta aikata ba.
“Don sake nanatawa, babu dalilin da Hukumar za ta musanta kamawa da kuma tsare waɗanda take zargi da aikata laifuka indai ta yi wani aiki da ya haifar da kama irin waɗannan mutane.
“Ba wani baƙon abu ba ne ga hukumomin tsaro da na kiyaye doka su kama su kuma tsare masu karya doka, ko waɗanda ake zargi da haka. Kamawa da tsare waɗanda ake zargi da aikata laifuka abubuwa ne masu tsari, kuma ana ci gaba da bitar su. A wasu sharuɗɗan, a kan tuhumi wasu lokaci bayan lokaci sannan a sake su, wasu kuma a kan ba su beli.
“Wasu da suke ƙarƙashin bincike a halin yanzu ko kuma tuni ma an fara kai su kotu ana tsare da su ne bisa umarnin Kotuna. Tsare mai laifi wani babban aiki ne na Hukumar, kuma tana yin wannan aiki ba tare da jin tsoro ba.
“Takan gudanar da wannan aiki yadda ya dace bisa tanadin tsarin tafiyar da dokokin manyan laifuka da kuma dokokin kiyaye rahotonnin sirri waɗanda suke wajibi don tabbatar da tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya.
“Amma, yana da muhimmanci a lura cewa waɗanda ake zargi da aikata laifuka dake hannun Hukumar ba a “azabtar da su lokaci bayan lokaci”. Wannan zargi Punch ko kowace kafar watsa labarai za ta yi abu ne kawai da suka yi zaton sa, kuma abu ne da ya shafi su waɗannan jaridu.
“Saboda haka, abin damuwa ne yadda Daily Trust da Punch suke amfani da kawunan labarai masu jan hankali kuma na son kai don ɓata Hukumar. Misali, a ɗaya daga cikin labaran Daily Trust na 31 ga Disamba 2019, ta bada rahoton cewa: “Bayan Watanni Huɗu, Iyali Sun Maka DSS a Kotu Bisa Ɓacewar Ɗan Gwagwarmaya”. Haka kuma, Jaridar Punch ta ranar 29 ga Disamba, 2019, ta yi amfani da “Labarun Baƙin Ciki Na Sauran Waɗanda Ake Tsare Da Su Ba Bisa Ƙa’ida Ba Yana Haifar Da Damuwa”.
“A waɗannan labarai masu rikitarwa, jaridun da ake magana sun yi wa Hukumar ƙarya. Jaridar Daily Trust ba ta ma yadda da wasu bayanai da ta samu daga Kwamandan Hukumar na Kaduna da kuma ‘Yan Sanda ba, waɗanda suka nuna cewa Hukumar ba ta tsare da IDRIS.
“Bugu da ƙari, jaridun ba su kawo wata hujja ko hujjoji ba waɗanda zasu tabbatar da abubuwan da suka rubuta cewa waɗanda ake zargi da aikata laifukan suna hannun DSS.
“Tsarin da waɗannan jaridu biyu da ake girmamawa fiye da sauran jaridu ya saɓa da ladubban aikin jarida. Matasayinsu da masu matsayi irin nasu suna nuna cewa a bar ƙasar nan ba doka, a bar ta cikin rikici, masu aikata muggan laifuka su ƙwace ta, yayinda ita kuma Hukumar ta tafi ta yi ta shirgar bacci don tsoron kar a ɓata mata suna.
“Hukumar ƙwararriya ce, kuma babbar mai ruwa da tsaki a tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya. Tsauraran dokoki ne ke saita ayyukanta. Tana sane da haƙƙin ‘yan ƙasa kuma, za ta ci gaba da gudanar da ayyukan da doka ta ɗora mata ba tare da jin tsoro ba. Za ta ɗora wannan aiki bisa tanadin doka, girmama haƙƙin ‘yan ƙasa da tallafa wa hukumomin da doka ta kafa.
“An yi imanin cewa Punch da Daily Trust ba za su yi wasu abubuwa da za su iya jefa tsaron ƙasa cikin haɗari ba, kuma saboda haka, za su yi aiki bisa kishin ƙasa da kuma lura da nauyin da yake kansu don tabbatar da zaman lafiya da oda.
“Hukumar ta sadaukar da kanta wajen haɗa kai da masu ruwa da tsaki, musamman kafafen watsa labarai. Amma tana so ta bayyana ɓalo-ɓalo cewa daga yanzu, ba za ta lamunci labarai na rikitar da mutane ba da kuma yi mata ƙarya, kuma a irin wannan yanayi, za ta yi amfani da matakan shari’a don ƙwatar haƙƙinta”, sanarwar ta lura da haka.