Magauta Ne Suka Zuga ASD Ya Kaini EFCC – Shehu Sani

111

Tsohon Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a Shekarun 2015 zuwa 2019 Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewar cinikayya ta kasuwanci ce ta shiga tsakanin sa da Alhaji Sani Dauda amma ba zambatar kudi ba, saboda haka ya yi mamaki ganin yadda ɗan kasuwar ya ɗauki matakin kai shi EFCC.

Sanata Shehu Sani ya ƙara da cewar matsayin sa na ɗan kasa nagari ne ya sanya shi karɓar goron gayyatar EFCC domin fayyace gaskiyar abin da ke faruwa tsakanin sa da Alhaji Sani Dauda mamallakin kamfanin motococi na ASD.

Tsohon Sanatan ya bayyana cewar babu shakka ya ziyarci ASD jim kaɗan bayan jami’an tsaro sun sako shi biyo bayan wani rikici da ya shiga tsakanin su da surukinsa a kwanakin baya domin ya jajanta masa.

A lokacin ne ASD ya shawarce shi da ya canza motar sa ƙirar Fijo zuwa sabuwar yayi ƙirar 508, inda suka yi ciniki akan Miliyan 7 da cewar zai yi biya biyu a cinikin.

Kuma nan take na bada Dala 25000 bayan wani ɗan lokaci na kara biyan Dala 13,000 da kuma Dala 12,000, inji Sanatan a ta bakin mai magana da yawun sa Suleiman Ahmad a zantawar sa da manema labarai a Kaduna.

An fara samun damuwa ne lokacin da ASD ya tafi aikin Umrah, kuma kafin ya bar Najeriya ya bada lambar asusun bankin ga Shehu Sani cewar ya saka sauran kudin da aka biyo shi, babban abin mamaki shi ne bayan dawowarsa daga Umrah sai ya yi ta kiran Sanatan ta waya ba kakkautawa, ba tare da sanin Sanatan ba ashe ASD ya hada wayar da suke yi da EFCC.

Sakamakon yawan kiran ASD ya sa Sanatan ya fahimci cewar da akwai matsala, wannan ne ya sanya lokacin da gayyatar EFCC ya zo mishi an bukaci ya bayyana ne ba ranar Alhamis 02 ga watan Janairu na sabuwar Shekara, amma sai ya kai kanshi a ranar Talata 31 ga Disambar shekara mai karewa.

Shehu Sani ya bayyana wannan abin da ya faru a matsayin wata zuga da makiyan shi suka yi wa ASD domin yunkurin cin zarafin shi da bata mishi suna a idanun mutane.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan