Yau Za A Haifi Yara 26,000′ A Faɗin Ƙasar Nan

63

Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF ya ce an yi kiyasin cewa yara 26,039 ne za a haifa a Najeriya a ranar sabuwar shekara.

Jariran da za a haifa a Najeriya za su zama kashi 7 ciikin 100 na jarirai 392,078 da za a haifa a fadin duniya a ranar sabuwar shekarar.

Najeriya dai ita ce ta uku a haihuwar da za a yi bayan Indiya da China.

Ga jerin kiyasin yawan yaran da za a haifa:

Indiya — 67,385
China — 46,299
Najeria — 26,039
Pakistan — 16,787
Indonesia — 13,020
Amurka — 10,452
Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo — 10,247
Ethiopia — 8,493


A kowace shekara, hukumar UNICEF na murnar sababbin yaran da aka haifa a ranar sabuwar shekara.

A shekarar 2018, yara miliyan 2.5 ne suka mutu a farkon watan da aka haife su a fadin duniya; kusan kashi ukun su a ranar da aka haife su ne suka mutu.

A Najeriya kusan yara 318,522 ne suka mutu a irin haka, ma’ana a farkon watan da aka haife su a shekarar 2018.

Cikin yaran, akasarinsu sun mutu ne sakamakon cututtukan da za a iya daukar mataki kansu da kuma matsalolin da suke bijirowa yayin haihuwa.

Bugu da kari, sama da yara miliyan 2.5 ne ake haihuwarsu a mace a duk shekara, inda dubu 400 daga Najeriya suke.

Rahoton BBC Hausq

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan