Duk da kasashe da dama na kokarin ganin sun rage yawan mata dake shiga sana’ar karuwanci, har yanzu matsalar na cigaba da yawaita a sassan duniya daban – daban.
Ga jerin kasashen duniya 10 da alkaluman kididdiga suka nuna cewa suna sahun gaba a yawan mata dake sana’ar karuwanci;
- 10. Kasar Thailand Kasar Thailand ta haramta karuwanci a hukumance duk da a aikace akwai karuwai a kasar.
Kiyasi ya nuna cewa akwai mata masu sana’ar karuwanci a cikin mutum 10,000.
- 9. Kasar Jamus (Germanny) Sabanin sauran kasashen nahiyar Turai, Jamus ta halasta tare da yin tsari ga masu sana’ar karuwanci a kasar.
Tun kusan shekarar 1200 AD kasar Jamus ta fitar da tsari ga masu sana’ar karuwanci. Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 49 a cikin mutum 10,000.
- 8. Kasar Malaysia Kasar Amurka ta yi wa kasar Malaysia bakar lamba a wajen safarar mutane da cin zarafin kananan yara. Watakila hakan ne yasa sana’ar karuwanci ta zama ruwan dare a kasar.
Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 52 a cikin mutum 10,000.
- 7. Kasar Brazil Sana’ar karuwanci ba haramun ba ce a hukumance a kasar Brazil, amma kuma doka ta haramta daukan karuwai domin aiki a Otal ko kuma jibge su a wani wuri.
Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 53 a cikin mutum 10,000.
- 6. Kasar China Kasar China ta haramta sana’ar karuwanci amma ana daukan hakan a matsayin karamin laifi.
Wasu masu bincike sun bayyana cewa akwai a kalla mata miliyan 10 dake sana’ar kasuwanci kuma suna taimaka wa kasar wajen samun kudin shiga.
Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 60 a cikin mutum 10,000.
- 5. Najeriya Babu wani birni a Najeriya da babu karuwai, kuma sana’ar karuwanci tana kara samun farin jini a Najeriya. Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 63 a cikin mutum 10,000.
- 4. Kasar Philippines Kasar Philippines tana bayar da wata shaida da ‘yammata masu sana’ar karuwanci zasu iya rataya wa a wuya domin saukin ganesu, kuma doka ta tilasta musu zuwa gwajin cututtuka da za a iya dauka ta hanyar jima’i (STDs).
Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 85 a cikin mutum 10,000.
- 3. Kasar Peru Sana’ar karuwanci ta halasta ga ‘yammatan da suka kai shekara 18 a kasar Peru matukar sun samu lasisi da takardar gwajin lafiya daga hukuma.
Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 102 a cikin mutum 10,000.
- 2. Kasar Koriya ta Kudu Duk da takunkumin da hukuma ta saka a kan karuwanci da kuma yawan kamen da ‘yan sanda ke yi wa karuwai, hakan bai hana karuwai cigaba da harkokinsu ba a kasar Koriya ta Kudu.
Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 110 a cikin mutum 10,000.
- Kasar Venezuela Matsin tattalin arziki ya jawo karuwar yawan masu shiga sana’ar karuwanci a kasar Venezuela, amma, duk da hakan, mafi yawan masu sana’ar karuwanci a kasar bakin haure ne.
Kiyasi ya nuna cewa akwai mata karuwai 119 a cikin mutum 10,000.
