Tsananin Yanayin Zafi Zai Sanya Ƙwari Su Cinye Abincin Duniya – Masana

232

Masu binciken kimiyya a kan kwari sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar za a samu asarar amfanin gona sakamakon karuwar zafin da za a fuskanta a nan gaba, kamar yadda gidan Rediyon BBC ya ruwaito.

Binciken da masana a Jami’ar Washington da bermont a Amurka suka gudanar, ya nuna cewa kwari a kasashen da ake tsananin zafi na yawan haihuwa a lokacin, lamarin da ke kara musu kuzarin cin abinci daga nan sai su far wa amfanin gona.


Rahoton ya ce za a yi asarar amfanin gona dangin hatsi da ya kai tan miliyan dari biyu a shekara guda a fadin duniya.

Ana sa ran yankuna masu sanyi a duniya su ne za su fi fuskantar matsalar, inda za a yi asarar kashi 25 zuwa 50 cikin 100 na amfanin gona dangin masara da alkama.


Masana kimiyar da suka gudanar da binciken kan kwarin sun ce ga duk ma’aunin zafi daya da ya karu, kwari za su cinye kusan kashi uku na shinkafa da masara da alkama da sauran dangin hatsi da aka noma a duniya.


Hakan kuma na nufin idan zafin ya rubanya zuwa maki biyu za a yi hasarar sama da tan miliyan 200 na hatsin.


Binciken masanan ya ce karuwar dumamar yanayi da za a fuskanta zuwa shekarar 2050 za ta haifar da yawan kwarin da za su cinye miliyoyin tan na abincin da aka noma a duniya ko da kuwa kasashen da suka tashi tsaye sun cimma burin rage hayaki da ke haifar da dumamar yanayi.


Sai dai masanan sun ce nau’in abincin da aka sauya halittunsu da kuma maganin kwari za su taimaka wajen yaki da barazanar kwarin.


Haka masanan sun yi gargadin cewa kwarin, za su fi morewa ne daga karuwan yanayin zafin da za a iya fuskanta. Kuma a cewar binciken barazanar, ba wai za ta shafi kananan kasashe ba ne, za ta shafi Amurka da Birtaniya da Faransa da China, inda binciken ya ce Amurka za ta yi hasarar kashi 40 na yawan masarar da take samarwa a shekara.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan