Kano Da Kaduna Sun Lashe Gasar Karatun Ƙur’ani Ta Ƙasa

300

Umar Kabir daga jihar Kaduna da Diya’atu Sanni Albdulkadir daga jihar Kano sun lashe Gasar Karatun Ƙur’ani ta Ƙasa Karo na 34, wadda aka kammala a jihar Legas ranar Juma’a.
Gasar, wadda Gidauniyar Gasar Karatun Ƙur’ani ta Najeriya da Cibiyar Nazarin Addinin Musulunci ta Jami’ar Usman Danfodiyo dake Sokoto suka shirya, da haɗin kan Ƙungiyar Musulmi ta Ƙasa, MSSN, Reshen Jihar Legas, Sarkin Musulmi, Muhammad Abubakar Sa’ad III, kuma Shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci, NSCIA shi ya buɗe ta ranar Juma’a, 27 ga Disamba, 2019.

Waɗanda suka lashe gasar sun samu sabbin motoci ƙirar Nissan Almera, kyaututtukan kuɗi da sauransu.

‘Yan takarar Gasar Karatun Ƙur’ani daga faɗin Najeriya ne suka fafata a gasar wadda take da ɓangarori shida da suka haɗa da: Ajin Haddar Izifi 60 da Tajwidi da Tafsiri, Haddar Izifi 60 da Tajwidi Zalla, Haddar Izifi 40 a Jere da Tajwidi.

Sauran ɓangarorin su ne Haddar Izifi 20 a Jere da Tajwidi, Haddar Izifi 10 da Tajwidi da Tangimi, sai kuma Haddar Izifi Biyu na Amma ko kuma Izifi Biyu s Jere A Ko’ina da Tajwidi.

An bada kyaututtuka ga sauran waɗanda suka yi nasara daga kowane ɓangare daga cikin ɓangarorin shida.

Jihar da ta ɗauki nauyin gasar ta zo ta shida, inda ta samu kyaututtuka shida daban-daban.

Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai-Elkanemi shi ya naɗa Gwarzon Sheka namiji, yayinda mai ɗakin mataimakin gwamnan Legas, Alhaja Khadijat Hamza ta naɗa Gwarzuwar Shekara.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Obafemi Hamzat, ya ce jihar za ta jure wa damar yin addini, kuma za ta ba dukkan mabiya addinai ‘yancin yin addininsu.

Ya ce hakan zai taimaka sosai wajen bunƙasa zaman lafiya da fahimtar juna, yana mai cewa da zaman lafiya ne kaɗai za a iya samun ci gaba.

Gwamna Mohammed Inuwa na jihar Gombe, wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Habibu Dahiru, ya ce Gasar Karatun Ƙur’ani za ta inganta haɗin kai da ‘yan uwantaka tsakanin al’ummar Musulmi, musamman duba da amfani da ‘yan takara ke samu ta ɓangaren samun kusanci ga Ubangiji da kuma a ilmance.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan