Kariya 15 Da Zogale Zai Bayar Fiye Da Duk Kwayar Asibiti

191

Hatta likitoci ma sun gano cewar an bar magani a gida an runtuma dawa, wato zogale kamar yadda ake ganinsa haka na da maganinuwa da ba sai an kai ga haɗiyar kwaya duk sanda ake ji ba daɗi ba, wanan abubuwan 15 su ke kunshe cikin zogale gandi mataimaki.
1 kariya da inganta fata da gashi
Man a ake tatsa a kwallon zogale na bada kariya ga fata da kyan gashi, yana hana ƙaiƙashewar gashin, bushewar fata da masu irrin ƙuraraji masu sa fata nuni ko dabbare-dabbare gami da cutukan saman fata.
2 maganin kurji mai zubar da ruwa
zogale na warkar da irrin ƙurji mai ɗurar ruwa a jiki. Wani lokaci kamar maruru da wani nau’i haka zogale bai barin su su lalata fata.
3 kariya ga hanta
Saɓanin yadda rake goge hanta, shi zogale yana magance ta ne yayin da ta kamu da ciwo kamar wanda wani sanadarin kariya cutar tubercular ke rattake ta, zogale na taimako ta warke.
4 taimako wajen kariya da magance sankara
zogale na dauke da sinadarin niazimicin dake hana yaɗuwar kwayoyin sankara da kariya ta musamman daga shi ciwon na Sankara da ya adabi mutane.
5 hana matsalolin ciki
zogale na hana murɗewa, kuburi, ciwon ciki da rashin narkewar abinci a cikin tumbin mutum. Wanda haka na haifar da matsalolin maƙil.
6 samar da kariya daga cututtuka
Salmonella, Rhizopus da Coli nau’in cutuka ne masu lahanta fata da cutukan ƙasbi, maƙero da makamantansu.
7 Tabbatar da kwarin ƙashi
zogale na magance cewon ƙashi wanda ke zuwa tare da yawan shekaru, sannan ya karawa ƙashi ƙarko da nagarta a jikin mutane masu ƙarcin shekaru.
8 magance ƙunar rai ko damuwa
zogale na haɓɓasa wajen kauwar da ciwon damuwa, gajiya ko makamancin haka.
9 bada kariya ga ilahirin kirji
zogale na tallafawa zuciya domin yi mata garkuwa daga afkawa cikin ciwo, sanan ya sa zuciya ta samu isasshar lafiya da bugu.

10 tallafi wajen warakar rauni
zogale na agaji ɓangaren warkar da ciwo da gyambo ko tabo.
11 magance ciwon suga (diabetics)
Zogale na rage yawan sinadarin glocose a cikin jini kana ya bunƙasa kwayar heamoglobin ta jini domin samun lafiya.
12 maganin ciwon hakki (asthma)
Zogale na huɓɓasa wajen magance cewon hakki na asthma da cushewar ƙirji ko makamancin su.
13 maganin ciwon koda
Yawan amfani da Zogale zai bada kariya domin kamuwa da ciwon ƙoda ko mafitsara. Don ko wanan na addabar mutane.
14 kariya daga hawan jini
Sinadaran isothiocyanate da niaziminin da Zogale ke ɗauke da na bada garkuwa wajen hana kaurarewar jijiyoyin jini wanda na haifar da hauwan jini.
15 Inganta lafiyar ido
zogale na inganta gani da ƙarfin idanuwa duba da irrin muhimman sinadarai da ya ƙunsa. Batun gani gara-gara ko yana-yana duk zai zama tarihi.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan