‘Yan Sanda A Kano Sun Cafke Wata Mata Da Ta Jefa Kishiya Da Jaririnta Rijiya

200

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta cafke wata mata da ake zargi da jefa kishiyarta da jaririnta ɗan wata 18 rijiya a ƙaramar hukumar Rano dake jihar.

Rahotonni sun ce wadda ake zargin, Hafsa Lawan ta gudu ta bar garin bayan da ta jefa kishiyar tata, Zuwaira Sani a rijiyar.

A cewar wani rahoton Freedom Radio, Misis Sani ta mutu jim kaɗan bayan da ‘yan sanda, waɗanda aka sanar da su afkuwar al’amarin suka garzaya da ita wani asibiti dake garin Rurum.

Amma jaririn Misis Sani, Mustapha Sani yana raye, yana kuma ci gaba da karɓar magani.

Da yake tabbatar da afkuwar al’amarin, Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an cafke wadda ake zargin ne, Misis Lawan bayan wani umarni da Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Habu Sani Ahmadu.

Mista Kiyawa ya ce tuni an kai wannan al’amari Sashin Kisan Kai na Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano dake Bompai don ci gaba da bincike.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan