Kashi 48 A Cikin 100 Na Ƙananan Yara Na Fama Da Matsananciyar Yunwa A Jihar Kano – Rahoto

93

Wani mamba a kwamitin inganta kiwon lafiya na masarautar Kano (KECCHD) Dakta Dayyabu Muhammad ya bayyana cewa kashi 48 bisa 100 na yara a jihar Kano na fama da matsananciyar yunwa.

Dayyabu Muhammad ya bayyana hakan ne a taron da KECCHD da asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya – UNICEF, su ka shirya domin samar da mafita game da matsananciyar yunwa da yara ke fama da ita a jihar Kano.

Ya ce an shirya wannan taro ne domin wayar da kan sarakuna da iyaye akan irin rawar da za su iya takawa wajen ganin an kawar da yunwa a jikin yara.

Muhammad ya kuma kara da cewa sakamakon binciken da KECCHD ta gudanar ya nuna cewa kashi 41.3 na yara kanana musamman ‘yan watanni shida zuwa shekara biyu a karamar hukumar Sumaila na fama da yunwa.

Sannan a karamar hukumar Bichi an gano cewa yara kanana kashi 38.1 na fama da yunwa a jihar.

Idan ba a manta ba a watan Satumbar 2019 ne gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta kashe akalla Naira biliyan 1.8 don ciyar da yara kanana dake fama da matsanancin yunwa a jihohi 18 dake kasar.

Shugaban sashen yaki da kawar da yunwa na ma’aikatar kiwon lafiya Chris Isokpunwu yace gwamnati ta kashe wadannan kudade ne tsakanin shekaru 2017 zuwa 2018.

Isokpunwu ya bayyana cewa sakamakon binciken da ma’aikatar kiwon lafiya ta gudanar a 2017 ya nuna cewa jihohi 18 a kasar nan na fama da matsanancin yunwa.

Ya ce a dalilin haka gwamnati ta tsaro matakai tare da hada hannu da Asusun kula da kanana yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) domin ganin ta kawo karshen wannan matsala a Najeriya.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan