Al’ummar Najeriya Da Kenya Sun Fi Ƙaunar Trump A Duniya – Bincike

175

Wani rahoto da cibiyar Pew Research Centre mai nazarce-nazarce ta fitar ya nuna cewa ‘yan kasar Kenya da Najeriya ne a gaba-gaba wajen kauna da gasgata al’amuran Shugaban Amurka, Donald Trump.

Cibiyar dai ta gudanar da wnai kwarkwayar kuri’ar jin ra’ayin mutane dangane da irin tinanin al’ummar duniya a kan shugaba Trump.

Kuri’ar ta gano cewa kaso 65 na ‘yan kasar Kenya da aka ji ra’ayinsu suna matukar kaunar Trump tare da imani da al’amuransa, inda kaso 58 na ‘yan Najeriya su ma suka kasance masu kaunar shugaban na Amurka.

‘Yan kasashen biyu dai na kaunar mista Trump duk da irin abubuwan rashin jin dadi da ya yi wa ‘yan Afirka a baya kamar bayyana Afirka da ‘masai’.

Kasashen guda biyu na Afirka dai na cikin kasashe 33 da aka gudanar da binciken a wajen Amurka a tsakanin watan Mayu da Oktoban 2019.

Nazarin na Pew ya kuma nuna cewa yankin kasashen Afirka yamma da hamada na nuna gamsuwa da Amurka.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne shugaba na farko daga kudu da saharar hamada da Amurka ta gayyata zuwa fadar White House a 2018.

Gwamnatin Donald Trump ta siyar wa Najeriya jiragen yaki guda 12 sabanin gwamnatin Barack Obama da ta ki sayar da makamai ga Najeriyar

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan