Tun Kafin Mata Su Waye: Annabin Rahama Ya Samar Musu Ƴanci – Craig

157

Wani Farfesa dan Amurka, Dakta Craig Considine, mai bin addinin Kiristanci, yace Annabin Muhammad SAW, ya nema wa mata ‘yancin su kafin su waye zuwa yanzu da suke gayun iyayi.

Dakta Craig Considine, shahararren marubucin alakar Musulunci da Kiristanci, malami ne a fannin ilimin sanin halayyar dan adam mai karantarwa a Jami’ar William Marsh Rice dake birnin Texas na kasar Amurka.

Ga duk ma’abota shafukan sada zumunta musamman Twitter, masu bin al’amuran da suka shafin addinai, suna cin karo da irin kalaman malamin akan Annabi Muhammad SAW.

Kasancewarshi mai binciken addini da neman kawo karshen tsangwama da kyara da akeyi wa musulmai musamman a kasar Amurka, a kowanne lokaci yakan fadi irin halayen Annabi Muhammad SAW wanda basu daga cikin manyan mabiya addinin Kirista kamarshi basa son fada.

Irin kalaman da ya dade yanayi akan kare fito da halayen ainahi na Annabi Muhammad SAW da nuna abinda yake kira da cewa “Shi masoyin annabi ne.”

Yace; A shekarar 629, Annabi Muhammad zai iya daukar fansa akan wadanda suka nuna masa tsana, amma baiyi haka ba, yace musu ‘God’ Allah mai yafiya ne kuma mai jinkai. Har ma yace musu kowa ya koma gidanshi.” – Dr Craig, Twitter, 8 Jan 2020

Hakan ne ake gayyatarshi zuwa taruka domin tattaunawa akan addinai tare da yada sakon cewa Musulmai da Kiristoci duk ‘yan uwan juna ne bisa a yacce yace duka Ubangiji daya ake bautawa.

A watan Disambar 2019, Dr Craig ya samu gayyata ta musamman daga Hadaddiyar Daular Larabawa inda ta kai shi ga zuwa babban masallaci nan na Sheikh Zayed Grand dake birnin Abu Dhabi.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan