Wasan Hamayya Na Birnin Madrid a Saudiyya

172

Wasan hamayya na birnin Madrid tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da Athletico Madrid ya tabbata amma fa a Saudiyya.

Shidai wannan wasan dazasu fafata atsakaninsu shine karon farko a sabuwar shekara ta 2020.

Itadai Athletico Madrid ta sami tikitin buga wasan karshen ne bayan ta doke kungiyar kwallon kafa ta Barcelona daci 3 da 2 awasan kusa dana karshe da suka fafata.

Ita kuwa Real Madrid ta lallasa Valencia daci 3 da 1 tun aranar Laraba.

Real Madrid da Athletico Madrid wasan hamayya ne na cikin gida tsakaninsu wato Madrid Derby, inda kungiyoyin kwallon kafan sun hadu agasar Laliga ta bana saidai wasan antashi kunnen doki babu ci tsakaninsu.

Akarshen makon nan zasu fafata wasan karshen na Super Cup tsakaninsu.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan