Ganduje Ya Rabawa Makarantun Furamare Kayan Aiki Na Miliyoyin Naira

160

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya raba kayayyakin koyarwa na makarantun Firamare ga kananan hukumomi guda 44 na Kano akan kudi naira miliyan 150 da kaddamar da raba kujeru da tebura guda dubu ashirin a fadin jihar baki daya.


Bikin rabon kayayyakin wanda ya gudana a harabar ma’aikatan Ilimi ta jihar Kano ya samu halartar manyan ƴan siyasa da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi.


Idan za’a iya tunawa dai gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da shirin ilimi kyauta kuma dole, duk da cewa masana a harkar ilimi sun kalubalanci lamarin a matsayin siyasa ce, la’akari da yadda malaman makarantun Furamare ke korafin rashin kayan aiki.

A karshe gwamna Ganduje ya mika cakin kudin na naira 100,000 ga malamai guda 200

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan