Rahotanni daga Oman na cewa Sarki Qaboos bin Said al Said ya mutu yana da shekaru 79 da haihuwa.
Sarki Qaboos bin Said al Said na Oman shi ne Sarki mafi dadewa a karagar mulki a daukacin Gabas ta Tsakiya.
Ya fara mulki tun shekarar 1970 bayan da ya yiwa mahaifinsa juyin mulki.

Sarki Qaboos bin Said al Said na da karfin fada a ji a Gabas ta Tsakiya da ke fama da rikici.

Hasali ma shine ya tabbatar da yiwuwar tattaunawa tsakanin Iran da Amurka, da ta yi sanadiyyar kulla yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran da a ka kulla a 2015.
To sai dai a na kuka da irin yadda ake hana masu fafutuka motsi a lokacin mulkin na sa.
An haifi Sarki Qaboos bin Said al Said 18 ga watan Nuwamban 1940, kuma ya yi kaurin suna a lokacin da ya kifar da gwamnatin mahaifinsa Sarki Said Bin Taimur da nufin kawo sauyin siyasa a Oman shekaru 50 da suka wuce.
[…] Muƙalar Da Ta GabataSarki Qaboos Na Oman Ya Rasu […]