Zinedine Yazid Zidane Jinin Kofi Ne?

134

Shahararren mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid kuma dan asalin kasar France wanda ya lashe kofuna rututu a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wato Zinedine Yazid Zidane ya sake lashe kofi akaron farko bayan dawowarsa ta biyu kungiyar kwallon kafan ta Real Madrid.

Inda shine mai horas war dayalashe kofi akaron farko tun bayan kamawar sabuwar shekarar 2020.

Inda kafin dawowarsa awancan lokacin ya lashewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid kofuna guda 9 wanda ya hadar da Laliga guda 1 da gasar zakarun turai guda 3 da gasar Spanish Supercopa guda 1 da gasar zakarun nahiyoyi guda biyu da kuma gasar Uefa Super Cup guda 2.

Shin yadda ruwan kofuna sukebin Zidane za a iya cewa shi jinin kofi ne?

Jaridar Labarai24 ta tattauna da Isma’il Abba Tangalash masani kuma mai fashin baki aduniyar wasanni dangane da cewa shi Zidane jinin kofi ne? Sai yace “Eh hakika Zidane jinin kofi ne ganin cewa kafin yabar Real Madrid ya lashe kofuna guda 9 daga fara horas da Madrid amatsayinsa na mai horas wa, wanda zakaga wasu masu horas war harsu gama horas wa bazasu taba lashe gasar zakarun turai ba amma shi 3 ya dauka ajere wanda bana tunanin cewar babu mai horas war dazai iya yin wannan ayanzu, bugu da kari tunda Zidane yabar Madrid basusake lashe kofi ba amma gashi daga dawowarsa yasake lashe ko idan ka tara da kofuna 9 na baya ya lashewa Madrid kofuna 10 cif sannan kaga tunda Zidane yake buga wasan karshe baitaba rashin nasara ba, sau 9 ya jagoranci Madrid awasan karshe kuma duk yayi nasara, kaga wannan ya nuna cewa Zidane jinin kofi ne”

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan