Sarki Sanusi II Ya Ce Osibanjo Ya Dinga Kallon Kansa Tamkar Ba Kano

231

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya yi maraba da ziyarar aiki na yini daya da mataimakin shugabankasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kai jihar Kano jiya Litinin.

Sarkin ya bayyana haka ne yayin da Osinbajo ya kai masa gaisuwar ban girma a fadarsa dake cikin birnin Kano, inda yace Osinbajo ya dauki jihar Kano tamkar gidansa, domin haka a kullum suna maraba da zuwansa.

Osinbajo ya kai ziyarar ne domin kaddamar da wasu manyan ayyuka guda biyu da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta aiwatar da suka hada da gadar sama ta Alhassan Dantata dake Sabon Gari da kuma gadar Tijjani Hashim dake kofar Ruwa.

Haka zalika Osinbajo ya gudanar da aikin sanya tubalin wasu muhimman ayyuka da gwamnatin Gwamna Ganduje za ta gudanar a jahar.

A jawabinsa, Sarki Sunusi ya bayyana farin cikinsa da ziyarar Osinbajo, inda yace hakan ya nuna muhimmancin jihar Kano ga gwamnatin tarayya.

Haka zalika Sarkin ya yabawa Gwamna Abdullahi Ganduje bisa ayyukan cigaban da yake gudanarwa a jihar Kano domin amfanin jama’a, inda ya bayyana ayyukan a matsayin cigaba da zasu inganta rayuwar jama’a tare da habbaka tattalin arzikin jihar Kano.

Shi ma da yake nasa jawabin, Farfesa Osinbajo ya jinjinawa Sarki Sunusi bisa kokarin da yake na tabbatar da zaman lafiya a jihar, sa’annan ya yabawa Sarkin bisa kokarin da yake yi na tabbatar da zaman lafiya a tsakanin mabanbanta kabilun jihar.

Daga karshe ya tabbatarwa Sarkin da cewa gwamnatin tarayya za ta cigaba da baiwa jihar Kano kulawa ta musamman wajen samar da ayyukan cigaba, fiye da sauran jahohin ƙasar nan.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan