Wani Yaro Ɗan Shekara 14 Ya Fara Koyarwa A Jami’ar Ƙasar Ingila

1000

Yasha Asley ya kasance malami mafi karancin shekaru, inda yake koyar da dalibai wadanda sun haifeshi. Haka kuma Yasha shima dalibi ne na digiri a jami’ar.

Yasha yana da matukar kwarewa a fannin lissafi. A cewar mahaifinsa, Yasha na yin iya bakin kokarinshi wajen ganin ya magance matsalolin lissafi. Tun yana dan karami Yasha ya iya lissafi, hakan ya sanya mahaifinsa yin iya bakin kokarinshi wajen ganin ya kware a wannan fannin.

Yasha yana da shekaru 12 ya fara karatun digiri na a jami’a, bayan ya kammala karatunsa na digiri, sai ya fara aikin koyarwa a wannan jami’ar.

A lokacin da Yasha ke da shekaru 8 a duniya, ya zama yaro na farko a duniya da ya fita da sakamako mafi daraja a fannin lissafi, duk kuwa da cewa Yasha bai halarci makarantar sakandare ba ko kwaleji.

Yasha yayi tsallake ne daga makarantar firamare zuwa jami’a domin fara karatun digiri na shi.

Yaron wanda har yanzu bashi da wani tunani akan abinda zai yi da rayuwarsa, amma ya bayyana shirinsa na zama Farfesa.

Yasha na matukar farin ciki wajen koyar da wasu mutane da ilimin da Allah ya bashi na lissafi.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan