Ko Sisin Kobo Ban Gada A Wajen Mahaifina Ba; Wahala Nayi Na Tara Dukiyata – Dangote

410

Fitaccen attajirin nan na nahiyar Afirika, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana wa ma nema labarai a wata tattaunawa da akayi dashi cewa bai gaji ko da sisin kobo a wajen mahaifinsa ba, inda ya ce shi ne ya wahala ya tara dukiyarshi.

Aliko Dangote wanda ke da dukiya wadda darajar ta takai dalar amurika biliyan 14, hakan ya sanya ya kasance na casa’in da biyar a masu kudin duniya, ya mallaki babban kamfanin siminti na nahiyar Afiriki da kuma matatar man fetur a Ibeju-lekki, kuma za ta kasance daya daga cikin manya-manyan matatun man fetur a nahiyar Afirka idan har ya kammala.

Attajirin ya bayya na cewa, ya fahimci mahaifinsa mai arziki ne amman wannan bai sa ya saki jiki yaki neman nashi ba.

A makonnin da suka gabata ne dai aka bayyana hamshakin mai kudin a matsayin wanda ya shiga cikin jerin masu kudi guda dari na duniya.

Attajirin wanda ya tashi a yankin arewacin Najeriya a kuma garin Kano ya kasance mutum na daya da har yanzu babu kamarshi a nahiyar Afirka.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan