Fitaccen dan wasan damben nan na kasar Amurka Muhammad Ali ya fadi wasu maganganu a lokacin da yake raye akan yadda zamu kaucewa aikata sabo.
Muhammadu Ali duk da yawan shaharar sa da kyawunsa da ke kewaye da shi ya nisanci alfasha da duk karfin sa.
Ya ce, “Bana shan taba amma ina ajiye kwalin ashana a cikin aljihu na. Lokacin da zuciyata ta karkata zuwa ga aikata wani zunubi, nakan dauko guda daya na kona domin naji zafinta a hannuna.
“Sannan na ce wa kaina, Ali, ba za ka iya jure wannan zafin ba, ta yaya zaka iya daukar zafin wutar lahira?”
Muhammad Ali ya kasance mutum mai addini, kuma bai gaza yin amfani da baiwarsa wajen fadakarwa akan addinin Musulunci ba. Bai taɓa ce wa mutane su zo su rungumi addinin Islama ba sai dai ya nuna musu kyawun addinin Islama.
Yayi magana game da kyawun Addinin Islama ga mafi yawan Amurkawa jahilai, ya fada masu game da Allah, ya sanar dasu labarin falalar dake cikin addinin Islama.
Ya Allah ka shiryar damu kuma ka nuna mana hanya madaidaiciya kuma ka tsaremu daga aikata zunubai.

[…] Muƙalar Da Ta GabataDa Ashana Nake Yawo A Aljihuna Domin Ta Dinga Tunatar Dani Azabar Wuta – Muhammad Ali […]
Munayimaku FATAN alkhairi a wannan sana’a taku ina dada Baku shawara Daku ringa fadin labarin Gaskiya
Ta hakane zamu gasgata labaranku Mungode.