Abba Kabir-Yusuf, ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓe gwamnan jihar Kano na 2019 ya mayar da martani ga hukuncin Kotun Ƙoli, wadda ta tabbatar zaɓen Abdullahi Umar Ganduje a matsayin halattaccen gwamnan Kano.
A wani hukunci da gaba ɗaya gungun alƙalan Kotun Ƙolin su bakwai suka amince da shi, wanda Mai Shari’a Nwali Ngwuta ya karanta a madadinsu, Kotun Ƙolin ta ce hujjojin da Mista Yusuf ya gabatar ba sa taimaki ɗaukaka ƙarar da ya yi ba, ƙarar ya gabatar da ita a kan hujja ɗaya tilo.
Amma a wata sanarwa da Mai Magana da Yawun ɗan takarar gwamna na PDP, Sanusi Dawakin Tofa ya fitar, Mista Yusuf ya yi zargin cewa alƙalai sun haɗa kai da “azzaluman dimokuraɗiyyar Najeriya” don yi wa al’ummar Kano fashin abinda suka zaɓa.
“Hukuncin yau kan gwagwarmayar zaɓen Kano ya tabbatar da haɗin baki da aka yi da ‘yan fashin zaɓe, waɗanda su ne azzaluman dimokuraɗiyyar Najeriya.
“Duba da tarin hujjoji da tawagar ƙwararrun lauyoyinmu suka gabatar, sai mutum ya kasa gane ya aka yi waɗannan wakilan zaluncin da na ƙa’idojin da ba na dimokuraɗiyya ba suka haɗa baki don yi wa al’ummar Kano fashin abinda suka zaɓa.
“To, mun ga mafi munin abinda za su iya yi, sai su jira hukuncin Allah Maɗaukakin Sarki, wanda ba za su iya guje wa ba”, in ji sanarwar.
[…] Da Ta GabataAzzaluman Alƙalai Sun Yi Wa Al’ummar Kano Fashin Zaɓe- Abba Muƙala Ta GabaYadda Mai Digiri Ya Koma Sana’ar Wanki Da […]