Gudun Abin Kunya Ya Sanya Na Kashe Budurwata – Mustapha Idris

122

Wani matashi mai suna Mustapha Idris, mazaunin karamar hukumar Ringim, a jihar Jigawa ya shaidawa manema labarai cewa ya kashe budurwarsa Nafeesat Hashim ne saboda gujewa barin abin kunya a garin su.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa Mustapha da Nafeesat saurayi ne da budurwa sai dai a zamantakewar su sun yi kusanta matuka da ya kai ga Mustapha ya dirkawa Nafeesat cikin shege.

Bayan cikin ya kai wata uku sai Mustapaha ya yanke shawarar kawai bari ya kashe ta gudun kada ta haihu ta jawo masa abin kunya a garin su.

Da yake suna zama a kusan gida daya ne sai Mustapha ya tafi bayan gari da Nafeesat inda a nan ne ya kashe ta.

Kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar Jigawa Audu Jinjiri ya bayyana cewa Mustapha ya amsa laifin sa.

Ko da muka gudanar da bincike mun gano cewa Mustapha ne ya kashe Nafeesat.

” Mustapha ya ce gudun ya bar abin kunya ne ya sa ya kashe Nafeesat kawai da dan dake cikin ta yadda gobe ba za ace ga dan sa da ya haifa da Nafeesat ba a aure ba.

Jinjiri ya kara da cewa sun iske Nafeesat kwance male-male cikin jini a inda ya jefar da gangan jikin ta.

Sai dai wata majiya ta bayyana mana cewa ita Nafeesat bazawara ce, ta taba yin aure.

Turawa Abokai

1 Sako

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan