Hukuncin Da Kotun Ƙoli Ta Yi Akan Zaɓen Kano Zalunci Ne – Abba Gida-Gida

125

Dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf ya bayyana hukuncin kotun koli na yau a matsayin wani hadin baki da cin zali da Kuma yi wa mulkin Demokradiyya danniya Kuma sun barwa Allah.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce “bisa la’akari da irin dumbin shaidu da aka gabatar da kuma gogaggun lauyoyi ya nuna irin halayyar zalunci ta yi wa jama’ar Kano fashi da makamin kuri’unsu.

Sai dai kuma gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana godiyarsa ga mahallici har ma ya nemi hadin kan yan hamayya domin ciyar da jihar Kano gaba.

Turawa Abokai

RUBUTA AMSA

Rubuta ra'ayinka
Rubuta Sunanka a nan