Hamshakin attajirin nan na nahiyar Afirka wato Aliko Dangote, ya ce duk lokacin da ya hadu da ƴan ƙasar nan, bukatarsu su ɗauki hoto kawai da shi a maimakon su tambaye shi kuɗi.
Aliko Dangote ya bayyana hakan ne a hirar da aka yi dashi a kan rayuwar sa, dukiyarsa da kuma shirin sa a nan gaba. Hirar wacce David Rubeinstein yayi da shi. Ya ce ya kan tuka kan sa tarr da zagaye birnin Legas a ranakun ƙ, arshen mako.

“Mutane ba su tambayata kudi idan na fito yawon shakatawata cikin ranakun mako amma su kan bukaci mu yi hoton selfie,” in ji shi.
Kamar yadda jerin sunayen manyan masu kudin duniya na Bloomberg Billionaires Index ya nuna, Dangote shi ne mutum na 95 mafi kudi a duniya.
Turawa Abokai